Kotu ta umarci Shugaban INEC ya kawo takardun takarar Tinubu na 1999 da 2023 a shari’ar Sowore

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta umarci Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan da ya kai mata takardun tsaya wa takarar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen gwamnan Legas na 1999 da na shugaban ƙasa na 2023 a shari’ar babban laifi na ɗan gwagwarmayar Omoyele Sowore.

Kotun ta umarci Amupitan da ya samar da takardun da bayar da shaida a shari’ar Sowore mawallafin ShaharaReporters, wanda Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) ta gurfanar da shi kan wasu wallafa a Soshiyal Mediya akan Tinubu. Ta aike da haka ne a wata wasiƙa mai taken “Subpoena Duces Tecum”, wadda aka gabatar da ita ga Amupitan kuma mai ɗauke da sanya hannun Mai Shari’a Mohammed Umar, a ƙorafi mai lamba FHC/CR/484/2025.

Musamman a ciki, an buƙaci INEC ta fitar da takardar Form CF001 ta Tinubu, ciki har da takardar ƙorafin ɓatar wasu takardu (affidavit), wanda ya bayar a matsayin ɗan takara a zaɓen gwamnan Legas na 1999. Haka kuma, ta buƙaci INEC ta miƙa mata Form CF001 na Tinubu na zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Wannan na zuwa ne bayan hukuncin kotun na ranar Litinin da ya bai wa masu kare ƙara damar tuntuɓar Shugaban na INEC da Joe Igbokwe, wanda tsohon sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC ne a Legas a matsayin shaida.

Yayin zaman na ranar Litinin, lauya mai kare Sowore, Ruben Adakole ya faɗa wa kotun cewa masu kare ƙarar suna yunƙurin kiran mutane biyun a matsayin shaidu. Akan haka ne Mai Shari’ar ya amince kuma ya bayar da umarnin a aike musu da takardar.

A wani ɓangare, kotun ta yi watsi da buƙatar Sowore ta neman a tilasta wa Akinlolu Kehinde, wato jagoran lauyoyin DSS ya zama shaida ga ɓangaren da aka shigar ƙara, yana mai cewa ba a tilasta wa lauyoyi bayyana wasu bayanai musamman ganin cewa haƙƙi ne akansu su kiyaye sirrikan waɗanda suke karewa.

Daga nan ne ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 11 ga Nuwamba domin bayyana shaidar wanda ake ƙara. Ana tuhumar Sowore ne kan kiran Shugaba Tinubu “Ɓarawo” a wani rubutu a Soshiyal Mediya.

By Babaji

Leave a Reply