
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris Malagi, ya sanar da dakatar da karɓar baki ɗaya kuɗaɗen lasisi ga kafafen yaɗa labarai har illa ma sha Allahu domin rage musu raɗaɗin matsin kuɗi da ke kan masana’antu yaɗa labarai a Nijeriya.
Idris ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Litinin, a lokacin da wata tawaga daga Kafar Yaɗa Labarai ta Ƙasa (BON) ƙarƙashin jagorancin Shugabanta, Cif Dakta Tony Akiotu ta kai masa ziyarar ban-girma bayan babban taronta karo na 82.
A wata sanarwa da mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, Rabi’u Ibrahim ya fitar bayan ganawar, ministan ya ce an ɗauki matakin ne bayan ƙorafi da BON ta yi kan hauhawar farashin gudanar da kafafen yaɗa labarai a Nijeriya.
Ya bayyana cewa, an dakatar da ƙare-ƙaren kuɗaɗen sannan an umarci Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NBC) da ta tabbatar da biyayya ga matakin da gwamnatin tarayyar ta ɗauka. Ministan ya kuma umarci Darakta-Janar na NBC da ya hanzarta yin nazari kan Dokokin Kafafen Labarai na Ƙasa domin tabbatar da tsarin gudanarwar ya dace da ci-gaban a masana’antar yaɗa labaran.
Game da matsalolin sadarwa na Digital Switch Over (DSO), ministan ya yi alƙawarin yin zama da masu ruwa da tsaki domin warware matsalolin da ake fuskanta a sashen sadarwa musamman bisa la’akari da muhimmancinsa ga ayyukansu na yau da kullum.
Da yake bayar da amsa kan buƙatar BON ta tilasta biyan kuɗaɗen tallace-tallace na tsawon kwana 45, ministan ya umarci Majalisar Gudanar da Harkokin Tallace-tallace ta Ƙasa (ARCON) da ta tabbatar da cikakkiyar aiwatarwa, yana mai cewa ma’aikatar labarai za ta yi aiki da masu ruwa da tsaki wajen samar da sauƙin lamuran kuɗaɗe gudanarwa a harkokin kafafen yaɗa labaran Nijeriya.
