An rantsar da alƙalai 375 da za su jagoranci kotunan ƙararrakin zaɓen 2027

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An rantsar da alƙalai 375 da za su jagoranci kotunan sauraron ƙararrakin zaɓen 2027 a Nijeriya, a wani yunƙuri na tunkarar taƙaddamar da ka iya tasowa bayan zaɓen.

An gudanar da bikin rantsar da alƙalan ne ranar Litinin a harabar shelkwatar Hukumar manyan Alƙalai da lauyoyi ta ƙasar, wato Body of Benchers Compleɗ da ke Abuja.

Cikin alƙalan da aka rantsar akwai mutum 138 waɗanda ke da ƙwarewa a kotunan sauraron ƙararrakin zaɓe, da kuma sabbi 237 da aka zaɓo daga kotuna da hukumomin shari’a daban-daban a faɗin ƙasar.

Da take jawabi a wajen taron, Shugabar Kotun ɗaukaka ƙara, Monica Dongban-Mensem, ta bayyana rantsar da alƙalan a matsayin wani muhimmin mataki na kare dimokuraɗiyyar Nijeriya.

Ta ce ingancin zaɓe bai tsaya ga jefa ƙuri’a kaɗai ba, domin tabbatar da adalci da warware taƙaddamar zaɓe cikin lokaci na da muhimmanci wajen kare haƙƙin jama’a.

Ta jaddada cewa ɓangaren shari’a na da alhakin tabbatar da fifikon kundin tsarin mulki, bin doka da oda da kuma ƙarfafa amincewar jama’a ga tsarin dimokuraɗiyya.

Dongban-Mensem ta kuma buƙaci alƙalan da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da adalci, tana mai tunatar da su cewa al’umma na sanya musu ido.

A ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Nijeriya, Shugabar Kotun ɗaukaka ƙara na da ikon kafa kotunan sauraron ƙararrakin zaɓe domin yanke hukunci kan taƙaddamar da ta shafi zaɓukan Majalisar Dokoki ta Tarayya, majalisun dokokin jihohi da na gwamnoni.

Rantsar da alƙalan na daga cikin shirye-shiryen ɓangaren shari’a na tunkarar ƙararrakin da za su iya biyo bayan babban zaɓen 2027.

By ukarofi

Leave a Reply