An horar da mutum 56 da za su koyar da ilimin AI ga malamai 3,202 a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ma’aikatar Ilimin firamare da sakandare ta Jihar Katsina, tare da haɗin gwiwar hukumar tarayyar Turai (EU) da UNESCO, ta kammala horo na kwanaki uku ga mutum 56 da aka zaɓa domin horas da malamai kan amfani da fasahar zamani wajen koyarwa da kuma basirar na’ura mai ƙwaƙwalwa (Artificial Intelligence AI).

An gudanar da bikin kammala horon a Makarantar Family Support da ke Katsina, ƙarƙashin shirin Expand, Integrate and Strengthen Systems (EISS), wanda aka tsara domin ƙarfafa ƙwarewa da inganta ayyukan malamai a fannin ilimi.

Kamar yadda bayani ya fito daga sashin yaɗa labarai ya fitar,Wannan shiri na daga cikin manyan tsare tsaren da Tarayyar Turai da UNESCO ke tallafa wa, domin bunƙasa ilimin amfani da fasahar zamani, inganta hanyoyin koyarwa da kuma shigar da fasaha cikin harkokin koyarwa a azuzuwa.

Jihohi shida ne ke cin gajiyar shirin, waɗanda suka haɗa da Adamawa, Bayelsa, Enugu, Katsina, Oyo da Plateau.

A yayin horon, malamai 56 da aka zaɓa daga cibiyoyin ilimi da ma’aikatu daban daban na gwamnati, sun samu ilimi da ƙwarewa ta aiki kan sababbin hanyoyin koyarwa ta amfani da fasahar zamani, musamman yadda za a yi amfani da basirar na’ura mai ƙwaƙwalwa wajen inganta harkokin ilimi.

Bayan kammala wannan horo, ana sa ran waɗannan ƙwararrun masu horaswa za su yaɗa ilimin da suka samu ga malamai 3,202 a faɗin jihar Katsina.

Daga cikin adadin malaman, 2,305 za su samu horo kai tsaye, yayin da sauran malamai 897 za su gudanar da horon ta yanar gizo, bisa tsarin koyon karatu da mutum zai iya gudanarwa da kansa a shafin horarwa na dijital da shirin ya tanada.

Haka kuma, za a gudanar da horon da za a yi wa malamai kai tsaye a rukuni biyu, a matakin ƙananan hukumomi, inda aka zaɓi ƙananan hukumomi takwas domin gudanar da shirin, tare da tabbatar da cewa malamai da dama sun samu damar cin gajiyarsa.

Manufar shirin ita ce shirya malamai domin rungumar sababbin hanyoyin koyarwa, inganta yadda suke gabatar da darussa, ƙara hulɗa da ɗalibai a cikin azuzuwa, tare da amfani da sababbin fasahohi, musamman AI, wajen samar da ingantaccen yanayin koyarwa da koyo.

Haka kuma, shirin na da burin ƙarfafa ci gaban ƙwarewar malamai a sana’arsu, tare da samar musu da ilimin fasahar zamani da zai taimaka musu wajen fuskantar sauye sauyen da ke faruwa a ɓangaren ilimi.

Gwamnatin Jihar Katsina, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa na ci gaba da aiwatar da sauye sauye a fannin ilimi ta hanyar zuba jari wajen inganta ƙwarewar malamai, bunƙasa koyon ilimi ta hanyar fasahar zamani da kuma samar da sababbin hanyoyin inganta ingancin ilimin firamare da sakandare.

Kammala wannan horo ya zama wani muhimmin mataki na shirin, yayin da ake shirin fara horas da sauran malamai ta hannun ƙwararrun masu horaswa 56 da suka kammala horon.

Ana sa ran wannan mataki zai faɗaɗa amfanin shirin EU–UNESCO zuwa makarantu da al’ummomi da dama a faɗin jihar, tare da ƙarfafa ƙwarewar malamai, bunƙasa amfani da fasahar zamani da kuma inganta koyarwa da karatun ɗalibai a Jihar Katsina.

By ukarofi

Leave a Reply