Omokri ya caccaki Peter Obi kan amfani da tsohon taken ƙasa a gangamin Legas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jakadan Nijeriya ga ƙasar Mexico, Reno Omokri, ya soki ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi da magoya bayansa bisa rera tsohon taken ƙasa a wani taron siyasa da aka gudanar a Legas.

Omokri, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce dokar ƙasa, taken ƙasa da Super Eagles alamomin ƙasa ne da suka dace su haɗa kan ‘yan ƙasa ba tare da la’akari da bambance-bambancen siyasa ba. Ya yi kira ga dukkan wani ɗan takara da ke neman al’umma su zaɓe shi a babbar kujera da ya riƙa nuna girmamawa ga cibiyoyi da alamomin ƙasar, yana mai gargaɗin waɗanda suka bijire musu a fili da gangan bai dace su yi tsammanin ‘yan Nijeriya su amince musu da jagoranci ba.

Wannan ya biyo bayan aukuwar wani al’amari ne a Legas, a lokacin da jam’iyyar NDC ke gudanar da gangami a yankin Oregun da ke Legas a ranar Alhamis, inda aka ga Obi, mambobi da magoya bayansu suna rera taken ƙasa da ya fara da ‘Arise, O Compatriots’, wanda tsohon taken ƙasar ne.

Da yake sukar al’amarin, Omokri ya kafa hujja da Sashe ne 24(a) na Dokar Ƙasa ta 1999 da aka yi wa gyara, wanda ke hukunta wa kowane ɗan Nijeriya yin biyayya ga dokar ƙasa da girmama manufofi, cibiyoyi, alamomi, da halastattun hukumominta.

Ya bayyana cewa, taken ƙasa ba abu ba ne na siyasa da za ƙi karɓa saboda bambance-bambancen ra’ayoyin siyasa, abu ne da yake a dokance ga kowane ɗan ƙasa ya wa biyayya, yana mai cewa Shugaban Ƙasa da Majalisar Dokokin Ƙasa ne kaɗai suke da ikon sauya taken ƙasa ba wasu mutane ko ƙungiyoyin siyasa ba.

Kazalika, Omokri ya ƙalubale da cewa ya za a yi Obi ya yi tsammanin ‘yan Nijeriya miliyan 235 su yarje masa gobensu muddin ba zai nuna girmamawa ga dokar ƙasa, taken ƙasa da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasa ba, yana mai cewa hakan ka iya jefa wasuwasi a zukatan ‘yan ƙasa. Nijeriya ta koma amfani da ainihin taken ƙasarta na da mai taken ‘Nigeria We Hail Thee’ ne a ranar 29 ga Mayu, 2024 biyo bayan ƙaddamar da Dokar Taken Ƙasa ta 2024 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi, wanda ke nuna ya maye gurbi ‘Arise, O Compatriots’ da ake amfani da shi tun a shekarar 1978.

By Babaji

Leave a Reply