Gwamnatin Raɗɗa ta aiwatar da ayyuka 1,019 a shiyar Daura

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta aiwatar da ayyukan ci gaba 1,019 a faɗin shiyyar Daura, inda kusan 131 a ƙaramar hukumar Baure, waɗanda suka shafi ilimi, lafiya, ƙarfafa tattalin arziki, ci gaban al’umma da jin daɗin jama’a.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin ziyarar girmamawa da ya kai fadar Sarkin Ban Daura kuma Hakimin Yanduna, Alhaji Muhammad Shazali Muhammad, a cigaba da gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓen Tinubu–Dikko/Jobe 2027 da ya fara a karamar hukumar Ɓaure a shiyar Daura.

Ya gode wa jama’a bisa tarba ta musamman, yana mai cewa fitowar maza, mata da matasa ta nuna karamcin al’ummomin yankin. Ya ce: “Duk lokacin da muka ziyarci wata al’umma, muna ganin yana da muhimmanci mu girmama hukumomin gargajiya, mu gana da dattawa da shugabannin addini, mu nemi albarkarsu da addu’o’insu, mu kuma nemi goyon bayansu domin ci gaban jihar mu.”

Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ba da fifiko ga kai ribar dimokuraɗiyya zuwa matakin ƙasa ta hanyar zuba jari a ilimi, lafiya, ƙarfafa tattalin arziki da jin daɗin jama’a. Ya ce ayyukan 1,019 sun haɗa da gyaran makarantu, cibiyoyin lafiya, shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arziki da tallafin jin daɗi a Baure.

Ya kuma bayyana cewa shugaban ƙaramar hukumar Ɓaure ya aiwatar da kusan ayyuka 300 tun bayan hawansa mulki, yana mai nuna rawar da ƙananan hukumomi ke takawa wajen isar da ci gaba ga al’ummomi.

A kan shigar al’umma, Gwamnan ya ce gwamnati ta kafa shirin ci gaban al’umma (CDP) domin al’ummomi su gano tare da ba da fifiko ga ayyukan da suka fi buƙata. Ya ce: “Mun kafa Shirin ci gaban al’umma domin tabbatar da al’ummomi sun shiga wajen gano da aiwatar da ayyukan da ke magance buƙatunsu na gaggawa.” Ya ƙara da cewa shirin ya bai wa sarakuna, shugabannin addini, iyaye da masu ruwa da tsaki damar kai tsaye wajen tantance fifikon ci gaba da aiwatar da ayyuka.

A kan hukumomin gargajiya, Radda ya ce gwamnatinsa ta ɗaga Hakimai zuwa matsayi na biyu (second-class), ta inganta matsayin Dagatai, sannan ta gabatar da alawus na wata-wata ga Dagatai a faɗin jihar. Ya kuma bayyana cewa an sanya Limaman Jumu’a 2,555, tare da mataimakansu da masu taimaka musu, a kan alawus na wata-wata, a matsayin yabo ga gudunmawar da shugabannin gargajiya da na addini ke bayarwa ga zaman lafiya, kwanciyar hankali, ci gaban al’umma da kiyaye al’adun gargajiya.

Gwamnan yace a matsayinsa na mai gudanar da yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya nemi goyon baya ga dukkan ‘yan takarar APC a zaɓe mai zuwa, yana mai addu’ar a samu zaɓe na lumana da nasarar aiwatar da shirye-shiryen gwamnati.

Tun da farko, Sarkin Ban Daura kuma Hakimin Yanduna, Alhaji Muhammad Shazali Muhammad, ya yaba wa gwamnatin Radda bisa shiga tsakani a ilimi, lafiya da ci gaban al’umma, ciki har da inganta cibiyoyin lafiya, samar da kayan aiki da magunguna da kuma gyaran makarantu da ke gudana. Ya ce yawan ɗaliban da suka shiga makaranta ya kai kusan miliyan ɗaya, yana mai bayyana hakan a matsayin ci gaba mai muhimmanci wajen faɗaɗa samun ilimi.

Sai dai, Hakimin ya yi kira ga gwamnati da ta shiga tsakani wajen kammala aikin makarantar sakandare a yankin, bisa wahalar da iyaye da ɗalibai ke fuskanta. Ya kuma nemi a samar da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana domin magance ƙarancin ruwa, da kuma inganta tsaro, musamman a kewayen makarantar da sauran wurare masu haɗari. Ya kuma nemi a ci gaba da kammala aikin da aka yi watsi da shi wanda ake zargin an fara ta mmhanyar SEMA ko shirin WASH, tare da gina magudanan ruwa domin magance ambaliyar ruwa a lokacin damina.

Haka kuma, Shugaban Ƙaramar Hukumar Baure, Hon. Saminu Suleiman Baure, ya gode wa Gwamna Radda bisa ziyarar da ya kai da kuma yadda gwamnatinsa ta girmama hukumomin gargajiya. Ya bayyana gangamin yaƙin neman zaɓen Tinubu–Dikko/Jobe a Baure a matsayin nunin shigar shugabannin siyasa, ‘yan jam’iyya, masu ruwa da tsaki na al’umma da mazauna yankin, yana mai tabbatar da ci gaba da jajircewar ƙaramar hukumar wajen shigar al’umma da tallafa wa shirye-shiryen gwamnati a yankin.

By ukarofi

Leave a Reply