Kungiyar masu buga bulo na fafutikar saukar farashin siminti domin masu ƙaramin ƙarfi — Babangida Ilyas

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Sakataren ƙungiyar Masu Sana’ar Buga Bulo ta ƙasa, reshen Yankaba, Kano, Malam Abdullahi Ilyasu Abdurrahman, wanda aka fi sani da Baban Gida, kuma mataimakin shugaban gidan bulo na Yankaba, ya bayyana cewa ƙungiyar tana da mambobi sama da 200 a Jihar Kano.

Ya ce ƙungiyar ba da daɗewa ba aka kafa ta, kuma har yanzu mutane na ci gaba da zuwa domin yin rajista.

Ya bayyana cewa a halin yanzu ƙungiyar tana fafutikar neman rage farashin siminti da duk wani abu da ake amfani da shi wajen ƙera bulo, domin sauƙaƙa wa masu son yin gini, musamman talakawa masu ƙaramin ƙarfi.

Babangida Ilyasu Abdurrahman ya bayyana hakan ne ga manema labarai a ranar Alhamis da ta gabata.

Haka kuma, ya ce ƙungiyar tana neman gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su tallafa mata, domin tana taimaka wa gwamnati ta hanyar ɗaukar dubban matasa aiki a ƙarƙashinta. Ya ce suna son a sauƙaƙa farashin siminti domin al’umma su samu damar yin gini.

Da yake magana kan sana’ar gidan bulo na Yankaba, Baban Gida Ilyasu ya ce wannan sana’a ce da ya gada daga mahaifinsa, wanda ya shafe shekaru 42 da kafa gidan bulo ɗin.

Ya bayyana jin daɗinsa kan yadda tsofaffin ma’aikata da abokan ciniki da suka yi hulɗa da mahaifinsa tsawon shekaru suke zuwa domin gaishe shi, tare da bayyana irin kulawar da mahaifinsa ya nuna musu, wadda suka kwatanta da ta uba ga ’ya’yansa. Ya ce wannan babban darasi ne da suke jin daɗinsa.

Ya ƙara da cewa a halin yanzu akwai ma’aikata sama da 50 da ke aiki a sassa daban-daban na gidan bulo ɗin, kuma suna kallon hakan a matsayin babbar nasara a rayuwa.

A ƙarshe, ya bayyana cewa suna ƙoƙarin ganin suna gudanar da aiki mai inganci domin gamsar da jama’a da abokan hulɗarsu na yau da kullum. Ya ce tashin farashin kayan aiki na damunsu, don haka suke ƙoƙarin samar da sauƙi ga jama’a.

Ya kuma ce suna aiki bisa ƙa’idar Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki ta ƙasa (SON), wadda ta tanadi cewa bai kamata a yi amfani da buhun siminti guda wajen ƙera bulo sama da 40 zuwa 45 ba. Saboda haka, ya yi kira ga ’yan ƙungiyar da sauran al’umma da su tsaya kan gaskiya da tsoron Allah a dukkan lamuransu.

By ukarofi

Leave a Reply