Kungiyar Mata Mu Koma Gona ta ziyarci gonar Sarman Integrated Farms

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Kungiyar mata mai suna Mata Mu Koma Gona, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Khadija Shaibu Ahmad ƙalu Gabari, ta jagoranci mata masu kiwon kaji da noma zuwa ziyarar ƙarin ilimi kan harkokin noma da kiwo a gonar Sarman Integrated Farms and Solutions Limited.

Gonar, wadda ta shahara wajen noman kayan amfanin gona, bishiyoyi, kiwon dabbobi, tsuntsaye irin su kaji, kifaye da sauran su, tana Agalawa kafin Agur, a kan hanyar Madobi, Jihar Kano.

A jawabinsa bayan karɓar baƙuncin ƙungiyar, manajan gonar, Adamu Gambo, tare da shugaban sashen kula da kifaye, Abdulrahman Adamu Saidu, sun bayyana farin cikinsu da wannan ziyara.

Manaja Adamu Gambo ya zagaya da ayarin matan zuwa wurare daban-daban na gonar, ciki har da inda ake kiwon kaji masu yin ƙwai, wurin tantance ƙwai, ɗakin kyankyasar ƙwai, wuraren kiwon kaji da kifaye, da sauran sassan gonar Sarman Integrated Farms.

A ƙarshe, Hajiya Khadija Shaibu Ahmad ƙalu Gabari ta ce burinsu da ƙudurinsu na bunƙasa noma da kiwon kaji, tsuntsaye, kifaye da sauran su ne ya sa suka kai wannan ziyara mai cike da alfanu.

Ta ce burinsu shi ne su kai matsayin da za su iya samar da ’yan tsaki da kansu, har ma su wuce yadda ake yi a Kudu, inda mata ke taka rawa wajen samar da su, kafin a kawo su Arewa. Ta bayyana cewa a kan fuskanci matsaloli yayin jigilar su a hanya.

Ta yaba wa shugabannin gonar, musamman babban manaja, Malam Adamu Gambo, kamar yadda wasu daga cikin ayarin ƙungiyar Mata Mu Koma Gona suka yi jawaban yabo ga hukumar gonar, wadda har gidan rediyon manoma take da shi a cikin gonar.

By ukarofi

Leave a Reply