Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Dr.Abdulmumin Kabir Usman, ya bayyana cewa samun nasarar hukumar hisbah ta Jihar Katsina ita ce nasararsa, yana mai jaddada cewa nasarar ba ta hukumar kaɗai ba ce, nasara ce ga addinin Musulunci da al’umma baki ɗaya.
Mai Martaba ya bayyana haka ne a lokacin da babban kwamandan hukumar hisbah ta Jihar Katsina, Sheikh Saifuddeen Yakubu Musa, ya kai masa ziyarar girmamawa a fadarsa.
Ziyarar na da nufin neman tubaraki da addu’o’i da shawarwari bisa sabon jagorancinsa na hukumar.
A jawabinsa Sheikh Saifuddeen Yakubu Musa, ya bayyana cewa, ziyarar sa na da nufin neman shiriya da jagoranci daga gare shi a matsayinsa na uba kuma jagoran al’umma.
Kwamandan ya kuma bayyana aniyar hukumar na yin amfani da shawarwarin da za ta samu daga masarautar wajen inganta ayyukanta da ƙarfafa kyakkyawar alaƙarta da masarautar Katsina.
Da yake jawabi, Mai Martaba Sarkin Katsina ya bayyana farin cikinsa da ziyarar, inda ya ce ya daɗe yana fatan samun damar zama da sabon kwamandan da tawagarsa domin tattauna hanyoyin da za a bi wajen inganta ayyukan hukumar.
Ya bayyana cewa aikin hisbah aiki ne mai buƙatar haƙuri, juriya, sadaukarwa da jajircewa, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kai da kyakkyawar sadarwa tsakanin jami’an hukumar da sauran hukumomin gwamnati domin samun nasara a ayyukansu.
Mai Martaba ya kuma gargaɗi jami’an hukumar da su guji duk wani abu da zai haifar da rarrabuwar kai, tare da tabbatar da cewa suna gudanar da ayyukansu cikin hikima, adalci da kyakkyawar mu’amala da al’umma.
Haka kuma, Sarkin ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ke ƙara ƙamari, musamman a tsakanin matasa da ƙananan yara, inda ya buƙaci hukumar hisbah ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kai tare da haɗa kai da sauran masu ruwa da tsaki domin shawo kan matsalar.
Bugu da ƙari, Mai Martaba ya ba da shawarar cewa hukumar ta duba yiwuwar faɗaɗa ayyukanta ta hanyar sanya kula da maƙabartu cikin muhimman ayyukanta, musamman ta fuskar kare filayen maƙabartu da tabbatar da tsaftar su.
Sarkin Katsina ya yi addu’ar Allah yaba sabon kwamandan da dukkan ma’aikatan hukumar nasara a sauke nauyin da aka ɗora musu, tare da tabbatar musu da cewa a shirye yake ya ci gaba da ba su shawarwari da goyon baya a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.
