Hon. Bilkisu Indabo ta shirya gasar mawallafa karo na farko a Kano

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Mai ba Gwamnan Jihar Kano shawara kan Ilimantarwa, Wayar da Kai da Haɗin Kan Al’umma, Hon. Bilkisu Yakubu Indabo, ta shirya gasar tsakanin mawallafa 12 da ke tallata ayyuka da manufofin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.

Indabo ta ce an shirya gasar ne bisa la’akari da muhimmancin rawar da mawallafan ke takawa wajen isar da saƙonni da kuma tallata ayyukan alheri da gwamnatin jihar ke gudanarwa.

Ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne domin ƙara wa mawallafan ƙwarin gwiwa da zaburar da su wajen zurfafa bincike tare da fito da sabbin hanyoyin tallata ayyukan gwamnan domin ci gaban jihar da al’ummarta.

Ta ce mawallafan na da tasiri wajen isar da saƙonni ga al’umma, tana mai cewa ofishinta ne ke da alhakin wayar da kan jama’a game da ayyukan gwamnati domin su san yadda ake amfani da kuɗaɗensu.

Ta kuma yi kira ga mawallafan da su ci gaba da wayar da kan al’umma game da ayyukan da ake gudanarwa ta hanyar nishaɗantarwa.

Indabo ta bayyana cewa wanda ya zo na farko ya samu kyautar naira 500,000, wanda ya zo na biyu kuma ya samu naira 300,000, yayin da wanda ya zo na uku ya samu naira 200,000. Sauran mawallafan sun samu kyautar naira 100,000 kowannensu.

Ta jaddada cewa babu wani ofishi a jihar da ya taɓa shirya irin wannan gasa tsakanin mawallafa, sai ofishinta, tana mai cewa za su ci gaba da shirya irin wannan gasa domin zaburar da mawallafan wajen yaɗa ayyukan gwamnan.

Ta taya waɗanda suka yi nasara murna, tare da ƙarfafa gwiwar waɗanda ba su samu matsayi na farko ba, cewa rashin samun nasara a wannan karon ba yana nufin ba su iya ba ne, domin wata rana su ma za su iya zama zakarun gasar.

A ƙarshe, ta bayyana cewa duk alkawuran da gwamnan ya ɗauka a lokacin neman zaɓensa ya cika su, tana mai cewa babu wani gwamna a ƙasar nan da ya gabatar da irin ayyukan raya ƙasa kamar na Gwamnan Kano, bisa la’akari da sauye-sauyen da ta ce ya kawo a jihar cikin ɗan lokaci.

Shi ma Shugaban ƙungiyar Mawallafan, kuma mai ba gwamnan shawara kan Walwala da Jin Daɗin Al’umma, Kwamared Abubakar Sani, ya ce an shirya gasar ne domin ƙara zaburar da mawallafan gwamnan da shugaban ƙasa, tare da ba su damar ƙara nuna basirar da Allah Ya hore musu wajen tallata ayyukan gwamnatocin.

Ya bayyana cewa an yi amfani da ƙwarewar mawallafan wajen tsara waƙoƙinsu da kuma yadda suke nuna damuwa kan al’umma a cikin waƙoƙin wajen tantance waɗanda suka yi nasara.

Ya kuma ja hankalin mawallafan da su ci gaba da amfani da basira da hikimar da Allah Ya ba su wajen yaɗa ayyuka da manufofin gwamnatin Kano da ta ƙasa.

Rabiu D. Malam, wanda ya zo na farko kuma shi ne sakataren ƙungiyar mawallafan, ya bayyana farin cikinsa bisa nasarar da ya samu.

Ya ce nasarar za ta ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen fito da ayyukan gwamnatin jihar ta hanyar basirar da Allah Ya hore masa.

Ya kuma yaba wa wadda ta shirya gasar, tare da tabbatar mata cewa za su ci gaba da tallata ayyukan gwamnatin APC.

By ukarofi

Leave a Reply