Rikicin diflomasiyya: Afirka ta Kudu ta gayyaci Jakadan Nijeriya, Fani-Kayode

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta gayyaci Babban Jakadan Nijeriya a ƙasar, Femi Fani-Kayode, domin yi masa bayani kan damuwar da ta bayyana game da wasu abubuwan da suka faru yayin miƙa takardun amincewa da naɗinsa ga Shugaba Cyril Ramaphosa, da kuma wasu kalaman da ya yi daga baya a kafafen sada zumunta.

Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa Darakta-Janar na Ma’aikatar Hulɗa da ƙasashen Waje da Haɗin Kan ƙasa da ƙasa ta Afirka ta Kudu (DIRCO), Zane Dangor, ya gana da jakadan Nijeriyar a ranar Talata, 17 ga Nuwamba, 2026, domin isar da damuwar gwamnatin ƙasar.

Wata sanarwa da Ma’aikatar Hulɗa da ƙasashen Waje ta Afirka ta Kudu ta fitar a ranar Talata ta ce Dangor ya tattauna batutuwan da suka shafi abubuwan da suka biyo bayan miƙa takardun amincewa da naɗin Fani-Kayode ga Shugaba Ramaphosa, da kuma kalaman da jami’in diflomasiyyar Nijeriyar ya yi daga baya a kafafen sada zumunta.

Jami’in na Afirka ta Kudu ya kuma tunatar da Babban Jakadan Nijeriya game da tanade-tanaden Mataki na 41 na Yarjejeniyar Vienna kan Hulɗar Diflomasiyya ta shekarar 1961, wanda ya tanadi cewa jami’an diflomasiyya su gudanar da harkokin aikinsu na hukuma ta hannun Ma’aikatar Harkokin Waje ta ƙasar da suka je aiki.

Dangor ya jaddada muhimmancin tabbatar da cewa duk wata sadarwa ta hukuma tana bin hanyoyin diflomasiyya da aka amince da su, ciki har da ta DIRCO.

Sai dai jami’in ya sake tabbatar da ƙudurin Afirka ta Kudu na kiyaye kyakkyawar dangantakar diflomasiyya da ta daɗe tana tsakaninta da Nijeriya, wadda ta ginu a kan mutunta juna, abota da haɗin kai.

Ma’aikatar ta ce Afirka ta Kudu na nan daram a ƙudurin ƙarfafa dangantakarta ta musamman da Nijeriya, tare da ci gaba da hulɗar diflomasiyya mai amfani, bisa ruhin haɗin kan Afirka da mutunta juna.

By ukarofi

Leave a Reply