Daga ABUBAKAR A BOLARI, Gombe
Majalisar Masarautar Arewarmu Duniyarmu African Chiefdom and Council ta naɗa Ambasada Alhaji Ibrahim Babalili Abdullahi, wanda aka fi sani da Jarman African, a matsayin Sarkin Hausawan Kano na majalisar.
An gudanar da bikin naɗin sarautun ne a Abuja, inda aka karrama wasu fitattun mutane daga sassa daban-daban na Afirka bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban al’umma.
Baya ga Babalili, an kuma naɗa Uboya Dr Yussif Iddrisu Madingo a matsayin Garkuwan Afirka (Kowa Naaso), Sheikh Ismail Abubakri Bamaiyi a matsayin Sarkin Malamai na Afirka, yayin da Dr Surajo AbdulKarim Kwami ya samu sarautar Sarkin Lafiyar Arewa.
Da yake jawabi a wajen bikin, shugaban majalisar, Mai Martaba Ambasada Alhaji Ibrahim Haruna, ya bayyana cewa an zaɓi waɗanda aka naɗa ne bisa irin gudunmawarsu ga al’umma, kishin ƙasa da jajircewarsu wajen samar da zaman lafiya.
Ya ce majalisar ta ɗauki wannan mataki ne domin amfani da sarautun gargajiya wajen haɗa kan al’ummomin Afirka, tare da ƙarfafa dangantaka tsakanin sarakuna, malamai, shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki.
Ambasada Haruna ya jaddada cewa sarautun da aka bayar ba wai don a ɗaukaka sunayen waɗanda aka naɗa ba ne, illa wata babbar amana da ke buƙatar sadaukarwa da yi wa al’umma hidima.
“Wannan sarauta ba ado ba ce kawai, babbar amana ce da nauyi a wuyansu. Muna son su zama jakadun alheri, zaman lafiya da haɗin kai a duk inda suke a nahiyar Afirka,” in ji shi.
Ya buƙaci sabbin sarakunan da su yi amfani da matsayinsu wajen sasanta rikice-rikice, taimaka wa marasa ƙarfi, ƙarfafa zumunci da kare martabar al’adu da addinan al’ummomin Afirka.
Ya kuma bayyana cewa manufar majalisar ita ce gina Afirka mai haɗin kai, inda ba za a nuna bambanci tsakanin ƙabila, addini ko ƙasa ba.
A nasa jawabin, Ambasada Alhaji Ibrahim Babalili Abdullahi ya nuna farin cikinsa bisa karramawar da aka yi masa, inda ya gode wa majalisar bisa amincewa da ta yi da shi.
Sabon Sarkin Hausawan Kano na majalisar ya yi alƙawarin yin amfani da sabon matsayinsa wajen haɗa kan al’umma, inganta fahimtar juna da kuma bunƙasa zaman lafiya tsakanin al’ummomi.
Ya ce zai yi iya ƙoƙarinsa wajen sauke nauyin da aka ɗora masa, tare da tabbatar da cewa sarautar ta zama wata hanya ta ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin al’ummomin Afirka ba tare da nuna bambanci ba.
