2027: APGA ta amince da goyon bayan Tinubu a matsayin ɗan takararta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance APGA, ta amince da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓukan 2027, inda ta ci alwashin tara masa magoya baya don sake zaɓar sa.

Jam’iyyar ta sanar da haka ne a ranar Alhamis, yayin gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a Awka, Jihar Anambara, inda Gwamna Chukwuma Soludo da Shugaban APGA na Ƙasa, suka gabatar da tutar jam’iyyar ga Tinubu.

Wannan muhimmin ci-gaba ne da aka samu gabanin zaɓukan 2027 yayin da APGA, wadda ta saba bambanta matsayinta na siyasa a al’adarta, ta ayyana goyon bayan ga shugaban mai ci ɗan jam’iyyar APC.

Da yake jawabi a taron, Gwamna Soludo, ya ce an ɗauki matakin domin tafiyar da lamuran haɗin kan ƙasa, nasarori, haɗin kan tsarin tarayya da ƙarfafa alaƙoƙin siyasa a sassan Nijeriya.

Ya bayyana cewa, APGA ta yanke goyon bayan Tinubu ne don maslahar bambance-bambancen da ake da su a Nijeriya, yana mai cewa mambobin jam’iyyar za su tara masa ƙuri’a a zaɓen da ke tafe musamman bisa la’akari da amincewarsu ga tsare-tsaren jagorancinsa.

By Babaji

Leave a Reply