
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shahararren mawaƙin Hausa, Dauda Kahutu da aka fi sani da Rarara, ya tsinci kansa a mawuyacin hali a Masallacin Ƙasa da ke Abuja a ranar Juma’a sakamakon wani farmaki da wasu fusatattun matasa suka kai masa.
Mawaƙin, wanda ya shahara da waƙe ‘yan siyasar jam’iyyar APC, ya sake fitar da wata waƙar yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wadda ake kunnuwa a tarukan siyasa musamman a Arewa mai taken “Omologo”. Ya yi ta ne a lokacin da shugaban ya kai wata ziyara a Jihar Katsina a shekarar da ta gabata.
Al’amarin ya auku ne a lokacin da wasu fusatattun matasa suka kai masa farmaki duk da cewa yana tare da jami’an tsaro da ke sanye da kayan gida da masu kaki. Jami’an sun yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen daƙile harin, amma haka fusatattun suka cigaba da kai masa duka.
A wata ɗauka, an ga yadda mawaƙin ya cire hularsa mai ɗauke da rubutun yabon Tinubu. Haka kuma, bidiyon ya nuna yadda matasan suke jibgar sa da yaga masa kaya gabanin wasu masallata su shiga tsakani da janye shi daga wajen.
Duk da cewa ba a gano ainihin abin da ya sabbaba haka ba, al’amarin ya auku ne bayan mako guda da wasu matasa suka riƙa yin ihun kushe Shugaba Tinubu da harbin ayarin motocinsa a yankin Masallacin Shehu Shagari da ke Area 1, Garki a Abuja.
