Jarumi Gèrard Depardieu ya nemi afuwar matan da ya ci zarafinsu

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Fitaccen jarumin fina-finan Faransa, Gérard Depardieu, ya janye ƙarar da ya ɗaukaka domin ƙalubalantar hukuncin da aka yanke masa kan cin zarafin mata biyu, tare da bayyana nadamarsa da neman afuwar waɗanda abin ya shafa.

Jarumin mai shekaru 77 ya ɗauki wannan mataki ne ranar Litinin, 16 ga Nuwamba, 2026, a daidai lokacin da ake shirin fara sauraron ƙarar tasa, inda ya yanke shawarar janyewa maimakon ci gaba da fafatawa da hukuncin da kotu ta yanke masa a baya.

A watan Mayun 2025 ne wata kotu a Faransa ta same shi da laifin cin zarafin mata biyu da suka kasance cikin ma’aikatan da ke aikin shirya wani fim mai suna ‘Les Volets Verts’, wanda aka fara ɗaukar hotonsa a shekarar 2021.

Bayan samun sa da laifin, kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin watanni 18 a gidan yari, amma da dakatar da aiwatar da hukuncin. Ma’ana, ba a umarce shi da shiga gidan yari nan take ba, muddin bai karya sharuɗɗan da suka rataya da hukuncin ba.

Sai dai Depardieu bai gamsu da hukuncin ba, lamarin da ya sa ya ɗaukaka ƙara domin neman a sake duba shari’ar. Amma yanzu ya janye ƙarar, matakin da ya sa hukuncin farko ya tsaya daram.

A cikin bayanin da ya fitar, jarumin ya bayyana cewa ya fahimci cewa akwai bambanci tsakanin barkwanci da kuma abin da zai iya zama cin zarafi ga wani mutum.

Ya amince cewa a wasu lokuta yana amfani da kalaman batsa da barkwanci masu ɗauke da maganganun da suka shafi jima’i a wurin aiki, yana mai cewa yanzu ya fahimci cewa akwai iyakar da bai kamata a ƙetare ba.

Ya kuma miƙa abin da ya bayyana a matsayin sahihin neman afuwa ga waɗanda suka gamu da matsala sakamakon halayensa.

Depardieu dai ya kasance ɗaya daga cikin manyan jaruman fina-finan Faransa, inda ya fito a fina-finai sama da 200 cikin tsawon aikinsa da ya wuce shekaru 50. Ya samu karɓuwa sosai a ƙasarsa da kuma sauran sassan duniya saboda ƙwarewarsa wajen taka rawa.

Sai dai matsalolin shari’a da suka shafi zargin cin zarafin mata sun kasance babban ƙalubale ga martabar aikinsa a shekarun baya-bayan nan.

Haka kuma, wannan ba ita ce kaɗai shari’ar da ke gabansa ba, domin har yanzu akwai wata shari’a dabam da ta shafi zargin yi wa jaruma Charlotte Arnould fyade a shekarar 2018, zargin da ya musanta.

Matakin da ya ɗauka na janye ƙarar tasa ya sake tayar da muhawara kan yadda ake ɗaukar alhakin cin zarafi a masana’antar nishaɗi, musamman idan waɗanda ake zargi fitattun mutane ne da suka shafe shekaru suna samun karɓuwa a idon duniya.

By ukarofi

Leave a Reply