An cafke ɗan fashi bayan shekara takwas da sauya jinsinsa zuwa mace

Spread the love

Da alama wannan ɓarawo ya ɗauka cewa idan ya sauya kamanni, har abada jami’an tsaro ba za su ƙara gane shi ba! Tsawon shekara takwas yana ɓuya, har ya kai ga sauya salon rayuwarsa da kamanninsa, amma duk da wannan ƙoƙari, sai ga shi an gano shi. Ashe, mutum zai iya sauya tufafi, murya da kwalliya, amma ba lallai ne ya iya sauya sawun da ya bari a baya ba! Hausawa na cewa, “Ko an ɓoye gawa, wari zai tona ta.”

’Yan sanda sun kama wani ɗan fashi da ake neman sa tun shekara ta 2018, inda suka gano shi yana rayuwa a matsayin mace, sanye da wani nau’in tufafin da ya bambanta asalinsa gaba ɗaya.

Dubun mutumin mai suna Tugrul Basar ta cika ne kwanan nan a birnin Istanbul ta kasar Turkiyya, bayan an shafe shekara takwas ana neman sa kan lafin fashi.

Tugrul Basar dai an yanke masa hukuncin ɗaurin laifin fashi a lokacin da yake nuna kansa a matsayin jami’in gwamnati a shekarar 2010, amma ya yi nasarar tsere wa hukuncin ɗaurin shekara uku a gidan yari.

Hukumomi na ta neman sa tun daga wannan lokacin, amma kwatsam kwanan nan sai suka yi nasarar gano shi a shiyyar Kadıkoy da ke Istanbul, yayin wani gagarumin aiki na musamman.

Abin da ya sa batun Basar ya yi fice daga sauran waɗanda ake nema yayin gudanar da aikin neman masu laifin na musamman, shi ne ya kasance yana rayuwa a matsayin mace har na tsawon shekaru, inda ya ɗauki tsarin kamannin ’yar uwarsa, ta yadda iya gane shi zai yi wuya matuƙa.

Jami’an ’yan sanda ba su fayyace yadda suka gano Tugrul Başar ba, bayan shekaru da dama, amma an yi amfani da hanyoyin sa-ido, domin sa-ido kan iyalansa da kuma abokan hulɗarsa.

Ta haka ne suka sami damar gano cewa, akwai matasa mata guda biyu da ke zaune a gidan ’yar uwarsa, waɗanda dukkaninsu suke da kamannin ’yar uwarsa idan suka fito waje.

A cewar rahotannin ’yan sanda, sauyin kamanni na Basar ya zama mai tsanani sosai, ta yadda ba za su iya dogara kan hotunan fuskarsa na shekaru da suka gabata ba, domin gano shi.

Sun koma kan bin sahun macen da ke nuna kanta a matsayin ’yar uwarsa tare da tara shaidu har zuwa lokacin da suka samu tabbacin cewa shi ne yake yin shigar burtu.

Yayin da ’yan sanda suka kai sumame gidan Tugrul Basar tare da kama shi, sun kama shi yana dauke da katunan shaida na ’yar uwarsa, amma gwajin yatsa ya tabbatar da cewa shi ɗin ne.

Kodayake wasu majiyoyi suna ambaton sauyin tufafinsa da kamanninsa na mata, wasu suna iikirarin cewa, ya gudanar da tiyatar sauyin jinsi, domin samun wannan babban sauyi.

Tugrul Basar zai yi zaman hukuncin daurin gidan yari na maza, ko ta yaya yake bayyana kansa.

Kasancewar bai taba sabunta sunansa ko jinsinsa a hukumance ba a tsarin rajistar bil’adama na Turkiyya, za a gurfanar da shi ne bisa jinsin da ke kan katin shaidarsa, ba tare da la’akari da kamanninsa na fili ko yadda yake bayyana kansa ba.

By ukarofi

Leave a Reply