
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jagororin ‘yan bindiga a Jihar Zamfara sun gargaɗi shugabannin al’umma a Ƙaramar Hukumar Anka cewa ba za su bari a yi zaɓuka a ƙauyukansu ba muddin ba su yi biyayya ga umarninsu ba, kamar yadda wani sabon rahoto da wani Amurken kamfanin leƙen asiri na SARI Global ya bayyana. Rahotanni sun ce gargaɗin ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan bindiga suke yawan tare titina a sassan jihar, inda suke ƙone motoci da ƙaƙaba harajin Naira miliyan 50 akan ƙauyukan da ke Gundumar Ɗansadau ta ƙaramar hukumar da ya tilasta wa sama da mazauna 300 gudun hijira.
An bayyana haka ne a rahoton da kamfanin ya fitar akan nazarin halin tsaro na watan Oktoba da jaridar PUNCH ta samo a ranar Juma’a. Rahoton, wanda bai bayyana wanda ya jagoranci fitar da shi ba, ya ce Zamfara ta maye gurbin Borno a matsayin jiha mai mafi girman rashin tsaro a Nijeriya, wadda aka samu aukuwar matsalolin tsaro guda 69 da suka yi ajalin mutane 137 acikin watan.
A cewarsa, a ƙaramar hukumar Anka, wani jagoran ‘yan bindiga ya tara jagororin al’umma a Oktoba, inda ya faɗa musu cewa ba za su bari a yi zaɓe a ƙauyukansu ba, wanda ka iya tabbata muddin jami’an tsaro ba su ɗauki mataki ba. Sannan zai iya yin sanadiyyar ɗaiɗaita al’ummomin yankunan. Ya ce, barazanar ta nuna yadda halin ayyukan ‘yan bindiga ke cigaba da faɗaɗa a Zamfara daga kwanton-ɓauna wajen ƙaddamar da hare-hare zuwa salon karɓe iko da titinan sassan ƙananan hukumominta.
A cewar rahoton, wani ɗan bindiga ya fitar da wani bidiyo a ranar 13 ga Oktoba, inda ya yi barazanar ƙone dukkan wata mota da ke zirga-zirga a hanyar Gusau zuwa Ɗansadau. Bayan haka da kwana guda ne aka ƙone wata tirela a yankin Ɗansadau zuwa Magami, yayin da a ranar 16 ga Oktoba ‘yan bindiga suka tare titin tare da lalata motoci guda tara da yin fashi ga matafiya. Haka kuma, rahoton ya ƙara da cewa ‘yan bindigar sun yi barazanar kai hari akan ƙauyukan da suka gaza biyan harajin miliyan N50 yayin da aka gano ababen fashewa (IEDs) guda biyu akan hanyar Magami zuwa Hannu-Tara zuwa Ɗan-Sadau a ranar 8 ga Oktoba.
SARI Global ya ce ayyukan tare hanyar sun faɗaɗa zuwa sama da titi guda, yayin da ‘yan bindiga suka rufe hanyoyin zuwa Gurusu–Anka, Abare–Anka, Gusau–Magami, Kaura Namoda–Shinkafi, Mayanchi–Anka, Anka–Kuturu da Maradun–Danbaza da dai sauransu, yayin da suka cigaba da sace matafiya da kuma halaka direbobi da manoma. Rahoton ya bayyana cewa sojoji na iya bayar da kariya kaɗan yayin da wani kwanton-ɓauna a ranar 20 ga Oktoba a kusa da Gurusu ya yi ajalin rayukan mutane 20 a wata rakiyar ƙananan ‘yan kasuwa, ciki har da sojoji da ‘yan sanda. Sannan, ‘yan bindiga sun sake tare hanyar a ranar 31 ga Oktoba.
A cewar Hukumar Zaɓe Mai Zaman ta Ƙasa (INEC), Jihar Zamfara tana da ƙananan hukumomi 14 da rumfunan zaɓe 3,529. Sannan, mutane 1,952,060 ne masu rajistar zaɓe a zaɓen 2023, inda aka samu ƙarin wasu 313,115 masu rajista yayin da aka cigaba da rajista zuwa Agustan 2026.
A baya ma an yi ta samun matsalolin ƙaƙaba wa ƙauyuka biyan haraji a Ƙaramar Hukumar Zurmi da ke Jihar a lokacin zaɓen gwamnoni da ‘yan majalisar dokokin jihohi na 2023. Sauran ƙananan hukumomin jihar da suka fuskanci irin matsalar sun haɗa da Maru, Anka, Bukkuyum da Gummi a shekarar 2022 da 2025.
