Yadda Kwankwaso ya sa na rantse da Al-Ƙurani kan yarjejeniyar koma wa APC bayan shari’ar kotun 2023 – Gwamnan Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya zargi tsohon jigonsa na siyasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da karya alkawari akan wata yarjejeniya ta koma wa jam’iyyar APC bayan kammala zaɓen 2023, inda ya tirje akan cewa ya amsa wa shirin ne ta hanyar tabbatar wa Shugaban Bola Tinubu shirinsu na komawa jam’iyyar mai mulki.

Gwamna Abba ya yi wannan zargi ne a wata hira da BBC Hausa, inda ya bayyana cewa musamman Kwankwaso ya buƙaci ya (Abba) tunkari Shugaba Tinubu da tabbatar masa da cewa za su koma APC muddin shugaban ya janye daga tsoma baki a shari’ar zaɓen gwamnan Kano.

Ya ce, sun cimma yarjejeniyar ne bayan zaɓen 2023 a lokacin da aka ƙalubalanci nasarar da ya yi akan Nasiru Yusuf Gawuna na APC a kotu. A cewarsa, Kwankwaso ne ya farar da batun ƙulla yarjejeniyar kuma ya buƙaci Abban ya rantse da Al-Ƙurani cewa za su koma APC matuƙar aka bar shari’a ta yi aikinta ba tare da tsoma baki ba. “Kwankwaso ne da kansa ya aike ni ga Tinubu ya ce na faɗa masa cewa mun yi wannan alƙawari. Ya kuma buƙaci na rantse da ƙur’ani cewa idan Allah ya ba mu nasara, za mu koma tafiya a inuwa guda,” ya faɗa wa BBC.

Ya bayyana cewa, daga nan ne ya amsa wa yarjejeniyar kuma ya tabbatar wa Tinubu niyyarsu ta koma wa APC. Ya ƙara da cewa, Kwankwaso ya riƙa ganawa da Shugaba Tinubu da aike da tawagogi domin su tattauna yiwuwar haɗewa a jam’iyyar siyasa guda. Gwamnan, wanda ya koma APC daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a ranar 26 ga Junairu, 2026, ya ce bai butulce wa tsohon mai gidan nasa ba, saidai hakan da ya yi cika alƙawari ne da Kwankwaso ya jingine daga bisani.

Kazalika, ya yi watsi da cewa komawarsa jam’iyya mai mulki na da nufin kassara ‘yan adawa ko raba hankalin jama’a, yana mai cewa Kwankwaso na sane da tattaunawa a lokuta da dama da yarjejeniyoyin da aka yi gabanin sauya sheƙar tasa. Har ila yau, gwamnan ya magantu kan halin alaƙarsa da tsohon gwamnan Kanon, inda ya ce su kan yi hira akai-akai kuma musamman a wasu lokutan ya kan aika wa Kwankwason da saƙon gaisuwa.

Gwamna Abba ya kuma yi tsokaci kan rikicin aurensa da matarsa Zainab Musa Kwankwaso, wadda ‘ya ce a wajen Kwankwaso. A cewarsa, auren nasu ya faro ne a tsawon shekaru 20 da suka gabata, wanda aka samu albarkar haihuwar ‘ya’ya a cikinsa, saidai an samu wasu matsaloli a tsakaninsu, wanda ya kai ga an fitar da kayan matar daga gidansa kuma ta fice ba tare saninsa ba. Ya bayyana cewa, hakan bai sa ya yi tsokaci a kai ba har ma ya kan shaida wa ‘ya’yan nasu cewa mahaifiyarsu za ta dawo gida. Daga bisani sai kwatsam ya ji cewa ta shigar da ƙarar neman saki a wat kotun Abuja.

By Babaji