Shugaban THISDAY, Obiaigbena ya soki ‘yan sanda kan ayyana shi wanda ake nema bisa zargin barazana ga shugaban FirstBank

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban jaridar THISDAY da gidan talabijin na Arise, Nduka Obaigbena, ya caccaki matakin ‘yan sanda na ayyana shi a matsayin wanda ake nema bisa zargin barazanar rayuwar Darakta-Manaja na bankin FirstBank, Olusegun Alebiosu, inda ya bayyana hakan a matsayin “ƙoƙarin ɓata masa suna da ƙarfin iko” kuma ya tirje akan cewa bai samu saƙon gayyata ba daga ‘yan sanda ko wata hukumar tilasta biyayya ga doka ba.

Obaigbena ya bayyana haka ne a wata sanarwa da aka fitar a ofishinsa da ke Legas a ranar Laraba, bayan da Mataimakin Sufeto-Janar na Shiyya ta 2, Olohundare Jimoh ya sanar da cewa ana neman wasu mutane tara ciki har da shugaban yaɗa labaran kan dangantakarsu da wani bincike da ya ƙunshi barazana ga rayuwar Aelbiosu.

A ranar Talata ne dai Jimoh ya sanar cewa binciken ya biyo bayan kai wani ƙunshin alburusan da aka samu na 7.62mm guda biyu a ciki zuwa gidan shugaban bankin a Legas. An ce wani ɗan aike ne ya kai ƙunshin da sunan kyautar kayan sakawa. Jagoran ‘yan sandan ya bayyana cewa bincike ya nuna yadda cewa zargin barazana ta samo asali ne daga ƙoƙarin da FirstBank ke yi wajen dawo da biliyoyin kuɗaɗen rance da ake bin kwastomomin FirstBank.

A cewar Jimoh, an gayyaci kwastomomin banki guda 10 da wasu domin binciken a ranar 5 ga Nuwamba kuma aka umarci su amsa a ranar 12 ga Nuwamba. Saidai mutum guda ne kaɗai ya amsa gayyatar, lamarin da ya sa hukumar ta ayyana sauran a matsayin waɗanda ake nema ruwa-a-jallo, ciki har da shugaban na THISDAY. Waɗanda ake neman sune Ernest Azudialu-Obiejesi da Nnenna Azudialu-Obiejesi na Nestoil; Tope Shonubi na Sahara Group; Henry Kayode Ojogho na Broron Limited; Emmanuel Iheagwazi na Necit Nigeria Limited; Eze David na Energy Shield Petrochemical Limited; Emmanuel Orim da Victoria Orim na Luzen Plaza; da kuma Obaigbena.

Da yake tsokaci kan matakin, ofishin Obaigbena ya ce shugabansu bai samu wata takardar gayyata ba da ya shafi binciken daga ‘yan sanda ko wata hukuma a kowane wajensa. Ya bayyana cewa, Obaigbena a ‘yan makonnin nan yana tattaunawa da manyan jami’an ‘yan sanda har a ranar Alhamis, 19 ga Nuwamba, a lokacin da suka tattaunawa akan kafa ‘yan sandan jihohi kuma babu wata alama da ke nuna cewa ‘yan sanda na son ganin sa kan wani bincike.

Haka kuma, sanarwar ta ce Obaigbena ya riƙa tattaunawa da Alebiosu akan yadda za a dawo da basussukan da ake zargin THISDAY da Arise Television suna bin FirstBank, wanda aka soma tun lokacin da bankin ya aike da wasiƙar ba bashi ga kafafen labaran.

By Babaji