Daga AISHA ASAS
Fitaccen marubucin waƙa na Najeriya, Ogaga Ifowodo, ya yi kira ga masu shirya kyautar Nigeria Prize for Literature da su fara bayar da wani kaso na kuɗi ga marubutan da suka kai matakin ƙarshe amma ba su samu nasarar lashe babbar kyautar ba.
Ifowodo, wanda ya lashe kyautar ta shekarar 2026 da littafinsa na waƙoƙi mai suna ‘Why Does God Need a Gun’, ya bayyana cewa ya kamata a duba halin marubutan da suka yi ƙoƙari har suka kai matakin ƙarshe, amma ba su samu nasarar zama na farko ba.
A wata hira da aka yi da shi bayan bikin bayar da kyautar, marubucin ya bayyana cewa lokaci ya yi da kamfanin NLNG, wanda ke ɗaukar nauyin kyautar, zai fara tunanin samar da tukuicin ƙarfafawa ga sauran marubutan.
Ya ce: “Ina ganin lokaci ya yi da NLNG za ta samar da kyautar ƙarfafawa ga waɗanda ba su yi nasara ba. Wannan abu ya daɗe yana bukatar a yi shi.”
Ifowodo ya bayyana cewa kasancewar marubuta uku suna zaune a wuri ɗaya yayin sanar da wanda ya lashe kyautar na iya haifar da matsin lamba ga sauran biyun da ba su samu nasara ba.
A matsayinsa na wanda ya taɓa shiga gasar sau uku, ya ce ya fahimci irin yanayin da marubutan ke shiga yayin jiran sanar da sakamakon.
Saboda haka, ya ba da shawarar cewa a riƙa ba marubutan da suka kai matakin ƙarshe wasu kuɗaɗe, domin a nuna musu cewa ƙoƙarin da suka yi wajen samar da ayyukan adabi yana da muhimmanci.
A cikin shawarwarinsa, ya ambaci yiwuwar ba marubutan da suka shiga jerin dogon zaɓe (Longlist) tsakanin dala 3,000 zuwa dala 5,000 kowannensu, yayin da waɗanda suka kai matakin ƙarshe (Shortlist) za su iya samun aƙalla dala 10,000 kowannensu.
Ya yi wannan shawara ne tare da jaddada cewa ba wai kuɗi ne kaɗai ke nuna darajar marubuci ba, domin samun karɓuwa da karramawa kan aikin da ya yi ma na da muhimmanci.
Littafin Why Does God Need a Gun ya mayar da hankali kan labarin Leah Sharibu, ɗalibar makarantar sakandaren Dapchi da aka sace a Jihar Yobe, wadda rahotanni suka ce ta ƙi sauya addininta domin a sake ta.
Marubucin ya yi amfani da muryar Leah wajen bayyana wahalhalun da waɗanda suka fuskanci ta’addanci ke ciki, tare da haɗa labarinta da sauran waɗanda suka kurɓi irin wannan ƙaddara.
Wannan kira na Ifowodo ya sake buɗe wata muhimmiyar muhawara kan yadda ake tantance marubuta da kuma hanyoyin da za a iya ƙara musu ƙwarin gwiwa domin su ci gaba da samar da ayyukan adabi masu inganci.
