
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC) na reshen Arewa maso Gabas, Nafi’u Bala, ya sanar da shirinsa na fara yaƙin neman zaɓe a mako mai zuwa, yayin da ya bayyana ra’ayinsa na ɗaukar tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar a matsayin Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓensa idan ya dawo jam’iyyar bisa tsari.
Bala Gombe ya bayyana haka ne a wata hira, inda ya ce ba ya tsammanin kowane hare-hare akan muradinsa na tsaya wa takarar shugaban ƙasa domin ‘yan Nijeriya suna goyon bayansa da tafiyar siyasarsa. “Za mu fara yaƙinmu na neman zaɓen shugaban ƙasa a mako mai zuwa. Babu wanda zai farmake mu saboda ‘yan Nijeriya suna son mu,” inji shi.
Haka kuma, ya ce yana duba yiwuwar naɗa Atiku a matsayin darakta-janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen nasa muddin tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya koma ADC bisa tsari. Shirinsa na yaƙin neman zaɓen na zuwa ne yayin tsawon lokaci ana rikicin shugabanci tsakaninsa da tsagin ADC ƙarƙashin jagorancin su tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark.
A watan Satumban 2025 ne Bala Gombe ya tunkari Babbar Kotun Tarayya, inda ya nemi ta haramta wa Mark da wasu mambobin kwamitin jagorancin jam’iyyar na riƙo ayyana kansu a matsayin jagororin ADC a matakin ƙasa. Ƙorafin nasa ya ƙalubalanci zaman Mark a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa da naɗa Rauf Aregbesola a matsayin sakatare bayan Ralph Nwosu ya sauka daga muƙamin.
A wani hukunci da aka gudanar a ranar 5 ga Nuwamba, 2026, Mai Shari’a Peter Lifu ya soke jagorancin kwamitin riƙo na su Mark da dukkan wasu hukunce-hukuncen da suka aiwatar, ciki har da hanyoyin da aka bi wajen ayyana Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ga zaɓukan 2027.
Sannan, kotun ta yi hukuncin cewa wasiƙar murabus da aka yi zargin Bala ne ya sanya mata hannu, ba ta bayar da tabbacin cewa ya sauka a muƙaminsa ba na Maitaimakin Shugaban ADC na Ƙasa. Wannan al’amari ya biyo bayan korar Bala da wasu mambobin jam’iyya da tsagin su Mark ya yi a watan Afrilun 2026 kan zargin ayyukan zagon-ƙasa ga ADC.
