Gwamnatin Katsina ta fitar da sunayen ‘yan kwamitin mambobi tara don binciken dambarwar Sarkin Daura

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Katsina ta fitar da sunayen mambobin kwamitin mutum tara da aka kafa domin binciken zarge-zargen cin zarafi da aka danganta da Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, biyo bayan cece-kucen al’umma kan al’amarin. Gwamna Umar Dikko Raɗɗa na jihar ya amince da naɗa mutane tara a kwamitin binciken, wanda Alƙali Amiru Sanusi (mai ritaya) zai jagoranta a matsayin shugaba.

Sauran mambobin kwamitin sune Mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin sarauta, Usman Abba; Mai Shari’a Sadiq A. Mahuta (mai ritaya) kuma Galadiman Katsina; Kwamishinan Harkokin Addini, Isah Dabai; da Alhaji Lawal Aliyu Daura. Haka kuma, akwai Farfesa Halima Kabir ta Tsangayar Yaruka da Al’adu ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya; Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adun jihar, Dakta Bala Salisu Zango; da kuma Hajiya Khadija Abdulƙadir, wato mai bayar da shawara ta Masarautar Belgium akan Difulomasiyya.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Dakta Bala Zango ne ya sanar da haka a wata takarda, ranar Alhamis, inda ya ce an bai wa kwamitin ikon gudanar da bincike kan zarge-zargen, gayyatar dukkan waɗanda aka danganta da al’amarin da gano ainihin haƙiƙanin al’amarin ziyarar ‘yar yawon buɗe idon a fadar Sarkin.

Sannan, ana sa ran kwamitin zai yi nazari akan takardu masu alaƙa da zargin, rahotanni da wasu hujjoji da duba matakin nauyin basaraken da kuma bayar da shawarwarin ladabtarwa da wasu matakan gyara da suka dace. Kazalika, an umarci kwamitin ya gabatar da rahotonsa acikin wata guda daga lokacin da aka ƙaddamar da shi kuma zai fara aiki a nan take.

Akan haka ne gwamnatin jihar ta shawarci al’umma da su bar kwamitin ya gudanar da aikin da aka ba shi cikin ‘yanci ba tare da matsin da ba ya bisa doka. Ta kuma yi gargaɗin cewa ba ta tare da dukkan wasu ayyuka ko kalamai da ka iya haddasa hargitsi a binciken, tana mai tabbatar wa mazauna cewa za a yi adalci bisa sakamakon binciken da kwamitin ya damƙa mata.

Wannan al’amari ya biyo bayan zarge-zargen da wata baturiya ‘yar yawon buɗe ta yi akan sarkin cewa sarkin ya ci zarafinta a lokacin da ta kai ziyara fadarsa a mako na biyu na watan Nuwamba. Bayan cece-kucen al’umma da zargin ya janyo ne gwamnatin jihar ta sanar da dakatar da sarkin daga hada-hadar sarauta da kafa kwamiti domin binciken al’amarin.

By Babaji