Yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi: Nasara ta wuce kama masu laifi

Spread the love

Bayanin da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta yi cewa ta ba fiye da mutum 54,000 shawarwari tare da taimaka musu wajen murmurewa daga shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a cikin shekaru biyar da suka gabata, na ƙara fito da irin girman matsalar shaye-shaye da ke addabar Nijeriya. Haka kuma, wannan bayani ya sake tunatar da mu cewa yaƙi da miyagun ƙwayoyi ba zai tsaya ga kama masu safarar su da lalata wuraren da ake samar da su ba. Dole ne a kuma magance matsalolin ɗan adam da na zamantakewar da ke tattare da wannan annoba.

Da yake jawabi a babban taron kwamandojin rundunar hukumar da aka gudanar karo na biyu a birnin Benin, Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya yi wani muhimmin bayani a kan bambanci tsakanin masu amfani da miyagun ƙwayoyi da masu safarar su. Ya jaddada cewa dogaro da miyagun ƙwayoyi wata matsalar lafiya ce da za a iya magancewa, don haka bai kamata a riƙa ɗaukar duk wanda ke shan su a matsayin mai laifi kai tsaye ba.

Wannan matsaya ci gaba ce mai kyau da ya kamata al’umma su ƙara amincewa da ita, musamman a irin wannan yanayi da ake yawan kyamatar masu shaye-shaye maimakon ƙarfafa musu gwiwar wajen neman taimako domin su daina.

ƙididdigar mutanen da hukumar ta taimaka wa wajen murmurewa, tare da nasarorin da ta samu a ɓangaren yaƙi da miyagun ƙwayoyi, sun bayyana girman matsalar da kuma buƙatar ci gaba da ɗaukar matakan magance ta. A cikin wannan shekaru biyar ɗin, NDLEA ta kuma kama waɗanda ake zargi da laifuka sama da 76,000, ciki har da manyan dillalan miyagun ƙwayoyi 250. Ta ƙwace sama da kilogiram miliyan 16 na miyagun ƙwayoyi, ta lalata gonakin tabar wiwi da suka haura hekta 2,000, sannan ta samu nasarar gurfanar da mutane 16,691 da kuma tabbatar da hukuncin laifinsu a kotu.

Waɗannan nasarori, musamman a ƙarƙashin jagorancin Marwa, sun nuna irin sabon ƙudurin da hukumar ta ɗauka na tunkarar matsalar miyagun ƙwayoyi. Sai dai girman matsalar ya nuna cewa, duk da muhimmancin matakan tilasta bin doka, ba za a iya samun nasara a wannan yaƙi ta hanyar kame kaɗai ba. Kasancewar sama da mutum 54,000 sun buƙaci shawarwari da kulawar musamman domin murmurewa cikin shekaru biyar, ya kamata ya zama abin damuwa ga masu tsara manufofi, musamman dangane da yanayin zamantakewar da ke ingiza mutane zuwa shaye-shaye.

Haka kuma, ya kamata a fi mayar da hankali kan yadda shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ke shafar jinsi daban-daban. Ko da yake ƙididdigar da aka gabatar ba ta fayyace adadin maza da mata da suka amfana da shirin murmurewar ba, babu shakka matsalar dogaro da miyagun ƙwayoyi tana shafar jinsi biyu. Don haka, matakan da gwamnati ke ɗauka ya kamata su yi la’akari da irin matsaloli da buƙatun kulawa na musamman da mata masu shaye-shaye ke fuskanta, waɗanda a wasu lokuta ba a cika kula da su a tattaunawar da ake yi kan wannan matsala ba.

Ya kamata cibiyoyin kula da masu shaye-shaye su kasance da isassun kayan aiki da ƙwararrun ma’aikata domin samar da sauƙin samun kulawa, tare da la’akari da buƙatu na musamman na mata.

Abin da ya fi muhimmanci shi ne, Nijeriya ta tunkari matsalar daga tushenta ta hanyar ƙarfafa ƙoƙarin wargaza hanyoyin sadarwar masu safarar miyagun ƙwayoyi, gano masu samar da su da kuma katse hanyoyin kuɗaɗen da ke ɗaukar nauyin wannan haramtacciyar sana’a. Dole ne a ci gaba da kama manyan dillalai da ƙwace miyagun ƙwayoyin da suke safararsu, tare da tabbatar da cewa ana gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu yadda ya kamata. Bai kamata a bar manyan masu fataucin miyagun ƙwayoyi da abokan hulɗarsu su samu mafaka daga hukunci ba.

Haka nan, akwai buƙatar ƙarfafa tubalan tarbiyya da zamantakewar al’umma. ƙungiyoyin addini, hukumomin gargajiya, makarantu da iyalai dole ne su zama abokan hulɗa na gari wajen hana shaye-shaye, gano masu aikata hakan tun da wuri da kuma taimaka musu su murmure.

Musamman iyaye, ya kamata su ƙara sa ido kan irin abokan hulɗar ’ya’yansu da kuma sauye-sauyen halayensu. Makarantu ma su sanya shirye-shiryen wayar da kan ɗalibai game da illolin miyagun ƙwayoyi cikin ayyukansu na yau da kullum.

Bugu da ƙari, muna ba da shawarar kafa ƙungiyoyin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi waɗanda matasa za su jagoranta a matakin ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar, tare da samar musu da isasshen kuɗin gudanarwa. Irin waɗannan ƙungiyoyi za su iya taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan al’umma daga tushe, ba matasa shawarwari da taimakon juna, tare da gano waɗanda ke fuskantar matsalar tun kafin ta tsananta. Wannan zai fi amfani musamman a yankunan da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ke ƙara zama ruwan dare.

ƙananan hukumomi kuwa ya kamata su yi aiki tare da shugabannin al’umma da hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da ɗorewar waɗannan shirye-shirye.

A ƙarshe, ya zama wajibi a ci gaba da shirye-shiryen wayar da kan jama’a ta kafafen yaɗa labarai, domin ilmantar da su game da illolin shaye-shaye, hanyoyin samun magani da kuma hukuncin da ke tattare da safarar miyagun ƙwayoyi.

Shirin NDLEA na Yaƙi da Shaye-shayen Miyagun ƙwayoyi (WADA), wanda ya gudanar da shirye-shiryen wayar da kan jama’a sama da 17,000, ya samar da kyakkyawan tubali da ya kamata a faɗaɗa shi.

Nijeriya ba za ta iya lamunta da rasa wata ƙarni na matasa sakamakon shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ba. A jaridar Blueprint, muna yabawa NDLEA bisa nasarorin da ta samu, amma a ƙarshe, ba yawan kame ko ƙwace miyagun ƙwayoyi ne kaɗai za su zama ma’aunin nasarar yaƙin ba. Babbar nasara ita ce gina al’ummar da mutane kaɗan ke faɗawa tarkon shaye-shaye, miyagun ƙwayoyi kaɗan ke shiga hannun jama’a, sannan matasa da dama ke samun damar rayuwa mai amfani da ci gaba.

By ukarofi

Leave a Reply