Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) ta tabbatar da birane shida da za su karɓi baƙuncin gasar kofin ƙasashen Afirka ta 2027 (AFCON), wadda ƙasashen Kenya, Tanzaniya da Uganda za su shirya tare a karon farko a tarihin gasar.
Hukumar ta sanar da hakan ne yayin babban taronta na shekara-shekara da aka gudanar a Abuja ranar 21 ga Nuwamba, 2026. An tsara fara gasar a ranar 19 ga Yuni, 2027, inda za a kammala ta a ranar 17 ga Yuli, 2027.
Birane shida da aka zaɓa domin karɓar baƙuncin wasannin su ne Nairobi da ke Kenya, Dar es Salaam, Arusha da Zanzibar a Tanzaniya, sai Kampala da Hoima a Uganda.
Daga cikin ƙasashen uku, Tanzaniya ce za ta karɓi mafi yawan wasannin, inda za a gudanar da su a biranen Dar es Salaam, Arusha da Zanzibar. Uganda kuma za ta karɓi wasanni a Kampala da Hoima, yayin da Kenya za ta gudanar da dukkan wasanninta a birnin Nairobi.
Sai dai wasu biranen da aka yi la’akari da su tun a matakin shirye-shiryen gasar ba su samu shiga cikin jerin na ƙarshe ba. Waɗannan sun haɗa da Eldoret da Kakamega a Kenya, Dodoma a Tanzaniya da kuma Lira a Uganda.
A yayin gasar, za a yi amfani da filayen wasanni da ake da su a yanzu, tare da wasu sababbi da ake ginawa a ƙasashen uku.
A Kenya, ana sa ran gudanar da wasanni a filin wasa na Moi International Sports Centre da ke Kasarani, da kuma sabon filin wasa na Raila Odinga International Stadium, wanda aka fi sani da Talanta Stadium, dukansu a birnin Nairobi.
A Tanzaniya kuwa, filayen da za a yi amfani da su sun haɗa da Benjamin Mkapa Stadium da ke Dar es Salaam, da Samia Suluhu Hassan Stadium a Arusha. Haka kuma, za a gudanar da wasu wasannin a Zanzibar, inda ake da filin Amaan Stadium da kuma sabon filin wasa na Fumba Stadium.
A Uganda, za a yi amfani da filin wasa na Mandela National Stadium da ke Kampala, tare da Hoima City Stadium da ke birnin Hoima.
Kasashen Kenya, Tanzaniya da Uganda na ci gaba da shirye-shiryen karɓar baƙuncin gasar, domin tabbatar da cewa filayen wasanni da sauran muhimman abubuwan more rayuwa sun cika ƙa’idojin da CAF ta gindaya.
