2027: Ribaɗu ya yi gargaɗin Soshiyal Mediya da AI ka iya rura wutar rikici yayin da NBC ta sabunta kira ga gudanarwa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai ba wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribaɗu, ya yi gargaɗin cewa cigaba da amfani kafafen sada zumunta ba bisa tsari ba da fasahar artificial intelligence (AI) ka iya rura wutar yaɗa labaran bogi masu ruɗarwa, fargaba da rikici gabanin zaɓuka 2027, yayin da ake sabunta kira ga daidaita lamuran gudanar da Soshiyal Mediya a Nijeriya.

Ribaɗu ya yi wannan gargaɗi ne a ranar Alhamis a taron ƙasa akan tsaron zaɓe ga zaɓukan 2027, wanda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta shirya a Abuja. Ya ce, rikice-rikicen zaɓe da aka fuskanta a ‘yan kwanakin nan a sassan ƙasar sun nuna cewa akwai buƙatar a kimtsa da wuri, duba halin barazana da ɗaukar matakan kariya domin bai wa lamuran zaɓe kariya da ta dace daga dukkan wani farmaki ko rikici da ka iya bijirowa.

A cewar NSAn, tasirin Soshiyal Mediya da AI sun sauƙaƙe hanyoyin da wasu daga cikin al’umma suke amfani da su wajen yaɗa labaran ƙarya, kambama taruka, da haddasa fargaba a cikin yankuna, wanda hakan ke barazana ga tsaron ƙasa. “Wannan soshiyal mediyan babban haɗari ne. Yana samar da bayanan ƙarya, kambamawa, haddasa rikicin a tsakanin jama’a. Mutum guda, wani ƙaramin ɓera da ke zaune a wani ƙauye zai turo abin da zai janyo fitina. A mafi yawancin lokuta ƙarya yake yaɗawa,” inji shi.

Gargaɗin Ribaɗu na zuwa ne yayin da jami’an gwamnati da ‘ya’yan majalisa suke ƙara kira da a samar da dokar amfani da kafafen sada zumunta a Nijeriya, inda ita ma Hukumar Kula da Harkokin Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NBC) da buƙaci majalisar dokoki da ta ƙara mata ƙarfi domin gudanar da harkokin fagen soshiyal mediya.

By Babaji