
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Juma’a, 27 ga Nuwamba, 2026 Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun ya fara aiki a wa’adin mulki na biyu a wani bikin rantsuwa da aka gudanar a filin wasa na Osogbo da ke Osogbo, babban birnin jihar.
Alƙalin Alƙalan jihar, Adepele Ojo ne ya jagoranci rantsar da gwamnan yayin taron, wanda aka fara da misalin ƙarfe 11:35 na safe kima aka kammala a ƙarfe 11:39 na safe. Da fari an rantsar da Mataimakin Gwamnan, Kola Adewusi da misalin ƙarfe 11:20 gabanin rantsar da gwamnan.
Taron ya samu halartar manyan baƙi ‘yan siyasa da sarakunan gargajiya, ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima da tsohon gwamnan jihar, Adebisi Akande, wanda yaan daga cikin manyan da suke wajen taron a lokacin da Adeleke ya isa domin ƙaddamar da shi a wa’adin mulkin karo na biyu.
Haka kuma, akwai many jami’an gwamnatin jihar, ciki har da Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Wale Egbedun, da Sakataren Gwamnatin jihar Teslim Igbalaiye, waɗanda suna cikin ‘yan sahun fsrko da suka halarci wajen, inda bayan haka ne Shettima da Adeleke suka samu isa a tare.
Sauran mahalarta taron sun haɗa da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki; tsofaffin mataimakan gwamnoni Iyiola Omisore, Olusola Obada da Benedict Alabi; Alaafin na Oyo, Oba Akeem Owoade; Soun na Ogbomoso; Olubadan na Masarautar Ibadan, Oba Rasidi Ladoja; Oba Ghandi Olaoye; da Ma’ajin Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na Ƙasa, Diran Odeyemi, da dia sauransu.
