Nijeriya ta ƙaddamar da sabon shiri domin inganta tallafin jinƙai ga talakawa da masu rauni

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Nijeriya ta zauki matakan ƙarfafa tsarin tallafin jinƙai ga al’umma ta hanyar inganta haɗin gwiwa, musayar bayanai da kuma adana gogewar da aka samu wajen gudanar da shirye-shiryen taimaka wa talakawa da iyalai masu rauni.

ɗaya daga cikin matakan da aka ɗauka shi ne kafa cibiyoyin musayar ilimi da gogewa kan tallafin jinƙai a jihohin Adamawa da Borno, domin bai wa hukumomin gwamnati da ƙungiyoyin ci gaba damar musayar dabaru da bayanai, adana gogewar da suka samu da kuma inganta yadda ake gudanar da shirye-shiryen tallafi.

An tattauna batun ne a taron ƙasa kan musayar ilimi da gogewa game da tallafin jinƙai na shekarar 2026, wanda aka buce a Abuja ranar Litinin, 23 ga Nuwamba.

Taron na kwanaki uku, wanda aka tsara gudanarwa daga 23 zuwa 25 ga Nuwamba, ya samu goyon bayan Tarayyar Turai da Gwamnatin Jamus ta hannun Hukumar Haɗin Gwiwar Ci Gaban ƙasa da ƙasa ta Jamus (GIZ), tare da ƙungiyar Action Against Hunger Nigeria.

Taken taron shi ne, “Daga dabaru zuwa tsare-tsare: Sanya tsarin adana ilimi da koyo cikin hukumomi domin ƙarfafa tallafin jinƙai a Nijeriya.”

Masu shirya taron sun ce za a kuma tattauna hanyoyin farfaɗo da Cibiyar Musayar Ilimi kan Tallafin Jinƙai ta ƙasa, wadda Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar a watan Satumba na 2023.

Da take gabatar da jawabin buɗe taron, shugabar shirin GIZ mai tallafa wa ɗorewar tsarin jinƙai, shiga harkokin al’umma da ƙarfin tattalin arziki a Arewa maso Gabashin Nijeriya (SEPIN SUSI), Ana Vnambres, ta ce Nijeriya ta samu gogewa mai yawa sakamakon gudanar da shirye-shiryen tallafa wa al’umma tsawon shekaru.

Ta ce inganta tsarin tattara bayanai da adana ilimi zai taimaka wa hukumomi wajen rubuta darussan da suka koya, kare bayanan da suka tara da kuma amfani da hujjoji wajen yanke shawara mai inganci.

Vinambres ta bayyana cewa tsarin tallafin jinƙai ya ƙunshi fannoni daban-daban, ciki har da tallafin kuɗi da kayayyakin masarufi, ayyukan kula da al’umma, inshorar jinƙai da kuma shirye-shiryen samar da ayyukan yi.

Da take magana kan ci gaban da aka samu a matakin jihohi, Vinambres ta ce Adamawa da Borno sun fara aiwatar da hanyoyin shigar da tsarin adana ilimi da gogewa cikin ayyukan hukumomin gwamnatocinsu.

Ta ce shirin, wanda Tarayyar Turai da Jamus ke tallafawa ta hannun GIZ, ƙungiyar Action Against Hunger ke aiwatarwa tare da taimakon fasaha daga ƙungiyar Internationale Development Stories (IDS), ya taimaka wa jihohin biyu wajen samar da tsarin gudanarwa, horas da ma’aikatan da ke kula da bayanai da kuma kafa ma’ajiyar bayanai ta yanar gizo.

By ukarofi

Leave a Reply