Gwamnatin Kebbi ta yi watsi da ware wata ƙabila a matsayin ‘yar ta’adda

Spread the love

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce ba ta amince ba kuma ba alkhairi ba ne, a danganta jinsin ‘yan wata ƙabila a matsayin ɓatagari ko ‘yan ta’adda.

Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu, Yakubu Ahmed Birnin Kebbi ne, ya fayyace haka a taron manema labarai a Birnin Kebbi.

Kwamishinan yana sharhi ne akan umurni da kuma aiwatarda umurnin da shugaban ƙaramar hukumar Sakaba, Hon. Dauda Sakaba ya yi, na tilasta ma al’ummar Fulani su tashi daga yankin na Sakaba.

Yakubu ya ce ba wata ƙabila da za’a bai wa irin wannan umurnin ko a ware wani jinsin al’umma a tilasta masu barin gari dole.

Ya ce duk da yake ana samun kai farmaki ga waɗansu ƙauyuka da ke ƙaramar hukumar Sakaba, kuskure ne a ɗora laifin kacokan akan wata ƙabila guda ɗaya tak.

Kwamishinan ya ja hankalin al’ummar Jihar Kebbi, cewar irin wannan ɗabi’ar a wasu kasashe na duniya kamar Rwanda, inda aka ware wata ƙabila a matsayin ɓatagari, ya yi sanadiyyar kisan-kiyashi da akayi ma wannan al’ummar wadda aka ɗora ma baƙin-jini.

Yakubu ya ce ba daida ba ne a tsangwami wata ƙabila da cewar ita ce ke aikata duk laifuffuka ko ta’addanci.

Ya yi gargaɗin cewar Gwamnatin Jihar Kebbi ba ta amince da irin wannan hukumcin ba ko ra’ayi, na korar al’ummar wata ƙabila daga jihar, kamar yadda akayi ma Fulani a ƙaramar hukumar Sakaba.

A nasa sharhin da ya yi, shugaban majalisar dokokin Jihar Kebbi, Rt. Hon. Salihu Maikasuwa Dangoje, wanda ɗan asalin Sakaba ne, ya roƙi jama’a gafara dangane da kalamai da shugaban ƙaramar hukumar Sakaba Hon. Dauda Sakaba ya yi, wurin tilasta ma al’ummar Fulani su fice daga yankin Sakaba.

A zantawarsa da ‘yan Jarida a Birnin Kebbi, Rt. Hon. Dangoje, ya ce shugaban ƙaramar hukumar Sakaba ya yi kura-kurai a jawabinsa.

Ya ce Arewacin Najeriya gida ne ga al’ummar Fulani, kuma bai dace ba ko kaɗan a ayyana cewar ɗaukacin al’ummar Fulani abin ƙi ne, ‘yan ta’adda.

Shugaban majalisar yace, gaskiya ne, ƙaramar hukumar Sakaba ta sha fama da kai farmakin ‘yan ta’adda, yana mai cewar akwai baqin Fulani, sabbin fuskoki, da ke shigowa
zuwa yankin daga wasu sassa na Najeriya game da Kudancin ƙasar nan.

Rt. Hon. Dangoje ya ce, jama’a sun ga ƙaruwar satar mutane da kai ma garuruwa farmaki, saboda haka, al’ummomin Sakaba suka ce ba za su yi shiru ba har al’amura su ƙara tsanani.

Amma ya ce, ba dokacin Fulani suke ‘yan ta’adda ba, sai-dai wasu ‘yan kaɗan daga cikinsu, kuma ana samun irin waɗannan ɓatagari cikin kowace ƙabila ko jinsi.

Dangoje ya ce Fulani sun yi shekara da shekaru suna zaman lafiya a Yankin Sakaba, ya na mai bayanin cewar, duk matansa biyu a yanzu Fulani ne, sannan kuma, marigyayi mahaifinsa ya yi abokantaka da Fulani masu yawa cikin aminci da mutunci.

Saboda haka ya ayyana cewar al’ummar Sakaba dayya suke ‘yan uwan juna.

Ya tabbatar da cewar za su ci gaba da wanzar da zaman lafiya a Sakaba, sannan kuma, duk lokacinda aka gabatar ma Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, wani rahoto ko takardan-koke akan lamarin, wakilan Majalisar zasuyi gaskiya da adalci wurin kawo daidaito da zaman lafiya tsakanin duk al’ummomi da Kabilun dake ƙaramar hukumar Sakaba, a matsayinsu na masu sulhu da kawo zaman lafiya.

By ukarofi

Leave a Reply