DAGA MUKHTAR YAKUBU
Kamar yadda a duk ƙarshen shekara, makarantar Jammaje Academy wadda take koyar da ilimin Turanci tare da ɗaukar nauyi shirya finafinai take gudanar da taru a duk ƙarshen shekara, wanda a wajen taron ake haska fim ɗin da Shugaban Makarantar Malam Kabiru Musa Jammaje yake shiryawa ta ƙarƙashin kamfanin sa mai su Jammaje Production, a bana ma za a yi gagarumin taro a ranar 26 ga Disamba a babban ɗakin taro na Jami’ar Bayero da ke Kano inda za a gabatar da jawabai tare da nishaɗantar da mahalarta taron.
Kamar dai yadda Malam Kabiru Musa Jammaje ya shaida wa wakilinmu, ya ce “A taron na bana mun tsara abubuwa da dama fiye da yadda muka saba shiryawa a baya. Domin kuwa a bikin na bana akwai jawabi na musamman wanda babban malami a Jami’ar Bayero wato Farfesa A A Rasheed zai gabatar. Bayan shi kuma akwai sauran manyan baƙi da su ma za su gabatar da nasu jawabin.”
Ya ƙara da cewa ” Bayan haka kuma kamar yadda na faɗa maka akwai sabbin abubuwa. To a wannan za mu gabatar da sabon littafin da na rubuta mai suna ‘A Gentle Breeze” wanda yake ƙirƙirarren labari ne na Turanci. Ka san a baya an sanni da littattafai da dama na Turanci, amma duk na koyar da Adabin Turanci ne, a wannan lokacin ne na rubuta littafin ƙirƙirarren labari. Don haka ka ga wannan ya zamar da taron na daban.
Sannan kuma akwai fim ɗin Turanci mai suna ‘Nanjala’ wanda shi ma za a haska shi a wajen taron. Shi fim ɗin ya zo da wani salo na koyar da ɗalibai yadda za su koyi Turanci ne.
Shi fim ɗin an shirya shi ne don isar da saƙo tare da koyar da harshen Turanci ga ɗalibai da kuma ba su neman sanin sanin turancin har ma da masu neman kwarewa a harshen Turanci.
Amma dai saƙon da fim ɗin yake ɗauke da shi na wata ‘yar gwagwarmaya ce da ta samu kanta a fagen aikin jarida kuma take ƙoƙarin kwato ‘yancin mata da na masu ƙaramin ƙarfi, inda ta samu ƙalubale kala kala a rayuwar ta kuma daga ƙarshe ta cimma nasara.
Kuma wani abin sa zai bai wa mutane mamaki a fim ɗin yadda ya kasance mun yi amfani da jarumai na ƙasashen Afirika, domin waje muka fita don aikin fim ɗin ga kuma fitattun jarumai da muka dakko daga kudancin ƙasar nan, da kuma namu na Kannywood duk sun taka rawar gani sosai a cikin fim din .
Amma dai akwai wayar da kai sosai ga masu neman ilimi musamman a makarantar Jammaje Academy, domin idan ɗalibi ya zo makaranta, yana buƙatar ka zaunar da shi ka wayar masa da kai a kan yadda zai ci nasara a makaranta. To shi ya sa muke samar da duk wata hanyar da ɗalibi zai fahimci karatu ko da ba a aji ba to abin da fim ɗin ya ƙunsa kenan.
Kuma baya ga haka akwai mawaƙa da za su zo su bajekolin fasahar su, kamar su Mudassir Kasim, Sadi Sidi Sharifai, Abubakar Sani, Ado Gwanja da dai sauran su. Kuma za mu gabatar da taron ne a ranar 26 ga Disamba nan da muke ciki kamar yadda aka saba ɗaliban makarantar Jammaje Academy za su halarta daga rassan makarantar da muke da shi 35 a duk faɗin ƙasar nan, kuma ban da ma ‘yan makarantar har ma waɗanda za su zo su kalla, za su fahimci irin abubuwan da ya kamata su yi idan sun shigo makarantar.” inji Malam Kabiru Musa Jammaje.

