A daina ɓata mana suna a kafafen sadarwa – FUYODA

Spread the love

Daga WAKILINMU

Shugaban ƙungiyar Matasan Fulani ta FUYODA a Jihar Filato, Abubakar Yusuf Umar, ya yi kira ga ’yan Nijeriya, musamman masu amfani da kafafen yaɗa labarai, da su daina aibata sunan ƙabilar Fulani, suna kiran su da sunan ’yan ta’adda ko ’yan bindiga marasa son zaman lafiya.

Shugaban ya ce, al’ummar Fulani mutane ne masu son zaman lafiya da son cigaba, kuma a ko’ina suke an san su da riƙo da al’adunsu da kyawawan halaye da aka yi musu tarbiyya a kai kuma suka taso a ciki.

“A kowacce al’umma a na samun nagari da mugu, haka ma ko a cikin Fulani. Don haka kuskure ne a riƙa yi wa Fulani kallon ta’addanci ko marasa son zaman lafiya. Idan mutum ya aikata laifi ko ya karya doka, a ambace shi da laifinsa ba ƙabilar da ya fito ba.

AY Umar ya ƙara da cewa, “Ni da kaina na fuskanci ƙalubale mai yawa a kan wannan matsala ta rashin tsaro, an kashe min ’yan uwa da dama, kuma na yi asarar dukiya da dabbobi. Shi ya sa muka shiga wannan gwagwarmaya ta samar da zaman lafiya da tsaro a tsakanin al’ummar Fulani da maƙwaftansu.”

Shugaban na bayani ne a wajen babban taron Fulani na shekara-shekara da ƙungiyar matasan Fulani ta FUYODA reshen Jihar Filato ta kira, wanda aka gudanar a Jos, ƙarƙashin jagorancin Sarkin Fulanin Wase, Arɗo Sa’idu Maikano, wanda kuma ya samu halartar wakilan dukkan ƙungiyoyin fulani daga ƙananan hukumomi daban-daban na Jihar Filato da Jihar Bauchi.

Taron da aka yi wa laƙabi da Ranar Pulaku, ya mayar da hankali ne wajen tattauna ƙalubalen da al’ummar Fulani ke fuskanta a zamantakewar su da maƙwaftansu, da kuma irin gudunmawar da za su bayar ga cigaban al’umma ta fuskar siyasa da tattalin arziki.

An gabatar da bita akan rawar da Fulani za su taka a siyasance, harkokin ilimi da zaman lafiya, inda ƙwararru daga Hukumar Raya Ilimin Makiyaya ta ƙasa, da Hukumar Bunƙasa Cigaban Zaman Lafiya ta Jihar Filato suka gabatar. Yayin da Hon. Muhammad Aminu Tukur daga Jihar Bauchi ya gabatar da muƙala ta musamman a wajen taron.

An kuma ƙaddamar da shafin yanar gizo na musamman da ƙungiyar FUYODA ta ƙirƙiro, wanda zai riƙa samar da ingantattun bayanai game da gaskiyar halin rayuwar da al’ummar Fulani ke ciki, cikin harsunan fulatanci, Hausa da Ingilishi.

Sarkin Fulanin Wase, Arɗo Sa’idu Maikano wanda ya jagoranci ƙaddamar da shafin, ya ƙalubalanci al’ummar Fulani su yi amfani da kafafen watsa labarai da zaurukan sada zumunta yadda ya kamata, domin fahimtar da al’umma haƙiƙanin gaskiya kan zalunci da cin zarafin da ake yi musu, a maimakon su riƙa bari ana ɓata musu suna ba tare da sun fito sun kare kansu ba.

Ya ce, “Idan ba ka fito ka kare kanka ba, wasu da ba su san abin da ke faruwa ba, sai su ɗauka kai ne mai laifi. Idan har wani abu ya faru da baku ji daɗinsa ba, sai ku ma ku fito ta kafafen watsa labarai ku yi bayani don a saurare ku kuma a ji daga ɓangaren ku.”

By ukarofi