Rikicin Filato: Mu guji tunzura juna da mummunan zargi

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Sunan Jihar Filato ya sake shiga bakin duniya, musamman bisa lura da irin rahotannin da kafafen watsa labarai daban-daban ke yaɗawa a ciki da wajen ƙasar nan. Wasu rahotanni masu tsoratarwa da ɗaga hankali, ko dai saboda irin munanan hotunan da ake bugawa na gawarwaki da ƙonannun gine-gine, ko kuma irin zafafan kalamai na tsana da nuna ƙiyayya da ake rawaitowa daga mutanen da abin ya shafa, marasa daɗin ji. Ko kuma masu ƙarfafa gwiwa da ke bayyana hanyoyin da za a iya kawo ƙarshen hare-hare da kashe-kashe da ke faruwa a jihar. 

A makon da ya gabata mun tattauna kan ƙoƙarin da muka ce gwamnatin jihar na yi don shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi jihar a watannin baya bayan nan, tare da ba da wasu shawarwari don ƙarfafa harkokin tsaro a yankin da ma jihohin Arewa bakiɗaya. 

Tun bayan hare-haren da aka kai kan wasu ƙauyuka a ƙaramar Hukumar Bokkos, da ya janyo asarar rayuka da dama da dukiyoyi, rahotannin da ke fitowa daga jihar ba su da daɗin ji. Duk kuwa da ƙoƙarin da hukumomi suka ce suna yi don daƙile bazuwar rikicin da gano masu hannu kan wannan aika-aika. Harin da aka kai kan wasu yankuna na ƙaramar Hukumar Bassa, da nan ma aka ce an hallaka rayukan mata da ƙananan yara da dattijai masu yawa, ya sake tabbatar da fargabar da ake da ita kan lalacewar zamantakewa da cigaban zaman lafiya da aka samu a jihar a ’yan shekarun baya.

An samu dawowar zaman ɗarɗar da rashin yarda, da jifan juna da baƙaƙen zarge-zarge, da ƙaruwar ’yan gudun hijira da suka bar muhallansu saboda rashin tsaro. Kalamai masu haɗari da rashin cancanta na cigaba da fitowa daga bakunan manyan ’yan siyasar jihar da masu riƙe da muƙaman gwamnati, waɗanda saboda kare muradun siyasar su, suke ambatar sunan Fulani a matsayin waɗanda suke zargi da kai hare-haren da ke kashe musu mutane.

Tun daga kan kalaman Gwamnan jihar, Barista Caleb Mutfwang, da na Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Filato, Aleɗ Dewan, da wasu jiga-jigan ’yan siyasa irin su tsohon Gwamnan jihar, Jonah Jang, wanda kurarsa ta daɗe da kuka akan rashin iya magana ta natsuwa akan ƙabilanci. Kalaman su ga ’yan jarida da kafafen watsa labarai, ya nuna cewa, ƙabilar Fulani makiyaya su ne suke da alhakin kashe-kashe a jihar da kuma ƙoƙarin su na ƙwace ƙasa ko korar asalin ƙabilun jihar don su mamaye su. Suna masu zargin fitintinun da ke faruwa a jihar ba rikicin ƙabilanci ba ne kamar yadda wasu ke gani, har da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wani ƙullallen shiri ne na masu jihadi, don rusa addinin Kirista. 

Waɗannan kalamai da ba sabbi ba ne a duk yayin da wani rikici ya auku a jihar, bai kamata ana jinsu daga bakin shugabanni ba, waɗanda suke da alhakin sauke nauyin al’ummar da suka zaɓe su, da ma waɗanda ba su zaɓe su ba bakiɗaya. Domin kuwa kalaman suna iya tasiri a zukatan mabiyansu, da kuma angiza su wajen ɗaukar matakin ramuwar gayya kamar yadda ya riƙa faruwa a baya. 

Masana harkokin tsaro da zaman lafiya, na ganin batun ɗaukar fansa da ramuwar gayya na daga cikin abubuwan da ke daɗa ruruta rikicin da ke damun jihar tsawon shekaru. Rahotannin da ke fitowa daga jihar na nuni da cewa, mako guda kafin harin da aka kai ƙaramar Hukumar Bassa, shugabannin al’ummar Fulani na yankin sun yi zargin, wasu ’yan ƙabilar Irigwe da ke yankin sun kashe wani matashin makiyayi tare da yanke masa kai, suka tafi da kan da kuma wasu shanu fiye da 70 da suke kiwo. Amma daga bisani an samu dawo da shanu fiye da 50, yayin da sauran ke hannun waɗanda ake zargi da sacewa. Sai dai batun ya shiga hannun jami’an tsaro da ke ƙoƙarin shiga tsakani. 

Wannan ɗaya ne daga cikin kashe-kashen makiyaya da shanu da ake yi wa Fulani a yankin, ba tare da duniya ta sani ba, saboda rashin samun haɗin kai daga wajen ’yan jaridu da wasu masu faɗa a ji. Labaran irin kisan mummuƙe da ake yi wa Fulani a waɗannan ƙauyuka da dama ba sa fita ballantana har duniya ta sani ballantana a tausaya musu, a cewar shugabannin Fulanin. Amma da zarar an kai hari kan wasu ƙabilu daban sai a riƙa kururutawa da bayyana ƙarya da gaskiya, musamman wajen bayyana adadin yawan waɗanda aka kashe. 

Shekaru da dama a wannan rikici da ake yi a Jihar Filato, abin da yake yawan kawo ruɗani da damuwa a tsakanin jami’an gwamnati da jami’an tsaro shi ne batun aringizo wajen bayyana adadin mutanen da aka kashe. Yayin da a gefe guda za ka ji ana faɗar adadi mai yawa, a ɓangare guda kuma sai ka ji ana zargin jami’an tsaro da zabtare yawan mutanen. Ko da a farkon wannan wata lokacin da Babban Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu ya kai wata ziyara jihar, sai da ya gargaɗi jama’a da manema labarai game da faɗar adadin da ba na gaskiya ba. Ya ce, ana yawan zuzuta adadin mutanen da aka kashe, alhalin jami’an tsaro ba su tabbatar da hakan ba. 

A yayin da jami’an gwamnatin jihar da shugabannin rundunonin tsaro ke gudanar da tarukan shawarwari kan sha’anin tsaro, da ganawa da masu ruwa da tsaki, wani muhimmin abin da ya fi ɗaukar hankalin jama’a a jihar daga ɓangaren Musulmi da Kirista shi ne yadda za a kawo ƙarshen waɗannan kashe-kashe na mugunta da ƙeta. Babu wanda ke farinciki da zubar da jinin da ake yi, musamman yadda ake salwantar da rayukan waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba, kamar mata da ƙananan yara. Sannan kuma a fahimci cewa duka rai yana da muhimmanci, da ran Musulmi da na Kirista. Babu wanda ransa ya fi daraja, wani kuma in an kashe an kashe banza! 

Daga cikin jawabin da Gwamnan jihar Caleb Mutfwang ya yi wa jama’ar jihar ta kafafen watsa labarai, ya ƙarfafa buƙatar kowacce al’umma ta kafa rundunonin ýan banga masu ƙarfin da za su taimakawa jami’an tsaro, wajen tsare rayukan al’ummar su da yankunan su, tare da neman a cigaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai da bayyana musu sirrukan da za su taimaka musu a gano maɓoyar ɓatagari. Hana kiwo cikin dare ko yawo da shanu a motocin ɗaukar kaya cikin dare. Da kuma hana amfani da babura da daddare.

Ba a wannan kaɗai gwamnati za ta tsaya ba, yakamata ta cigaba da wayar wa da mutane kai game da muhimmancin zaman tare da girmama addini ko ƙabilar wani. ɗora dukkan wani laifin ta’addanci kan Fulani ba adalci ba ne. Yaɗa cewa Fulani na ƙaddamar da jihadin da Shaihun Usman ɗanfodiyo bai iya yi a jihar ba ne tun lokacin yaƙe-yaƙe, ba kalamai ne da za su kawo zaman lafiya ba. Tunanin cewa, za a kori Fulani ko wata ƙabila daga zama a wani yanki na jihar, babban kuskure ne da karya dokar ƙasa. Duk wani ɗan Nijeriya na da ’yancin ya zauna ya yi rayuwa a ko’ina a ƙasar nan, kuma su ma Fulani ’yan ƙasa ne. 

Sai dai duk da haka ba dalili ne da zai sa mu kawar da kai daga duk wani kuskure na ɗaukar doka a hannu da ake zargin Fulani da aikatawa ba. Ko haka ne ko ba haka ba ne, dole ne shugabannin Fulani su iya tsawatarwa mutanen su game da aikata duk wani abu da zai kawo rashin zaman lafiya ko lalacewar tsaro a duk inda suke ba a Jihar Filato kaɗai ba. A guji ɗora alhakin rikice-rikicen da ke aukuwa kan wani ɓangare na addini, domin haɗarin da hakan ke da shi ga samun nasarar zaman lafiya a jihar.

Wata sanarwa da ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) reshen Jihar Filato ta fitar mai ɗauke da sa hannun Sakataren ƙungiyar na jiha, Dakta Salim Musa Umar, ta buƙaci Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama tare da binciken wani Kefas Gyang Pam, wanda ya yi wani rubutu a shafin sa na Facebook yana nuna cewa, Musulmi ne tushen duk wata matsala da Jihar Filato ke fuskanta. Rubutun da ya harzuƙa al’ummar Musulmi a jihar, kuma ƙungiyar ke fargabar zai iya tunzura wasu, saboda shigar da sunan addinin Musulunci da ya yi cikin wannan mummunan zargi.

By ukarofi