A fim ɗin ‘Faliha and Falisha’ aka ba ni matsayin da babu wani furodusa a Kannywood da ya taɓa ba ni – Isa Ballo Ja

Spread the love

DAGA MUKHTAR YAKUBU

A satin da ya gabata ne aka kammala ɗaukar sabon shirin fim ɗin ‘Faliha and Falisha’ wanda kamfanin shirya finafinai na Today’s Life Nigeria Limited na jaruma Mansurah Isah suka ɗauki nauyin shiryawa.

Fim ɗin wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan finafinai da ita Mansurah Isah ta ɗauki nauyin shiryawa. An shafe kusan sati biiyu ana aikin tare da manyan jaruman Kannywood da suka haɗa da Mommy Gombe, Isa Ballo Ja, Timmah Makamashi da dai sauransu.

Matashin mai bayar da umarni Darakta Isah Alolo shi ne ya bada umarni yayin da ita kuma Mansurah Isah ta kasance babbar mai shiryawa.

Wakilinmu ya halarci wajen ɗaukar fim ɗin a lokacin da ake gudanar da aikin a wasu sassa daban daban na cikin birnin Kano da kewaye, inda a farko ya ji ta bakin Darakta Isah Alolo kan yadda aikin yake gudana, inda ya bayyana masa cewa,

“Gaskiya aiki yana tafiya yadda ya kamata saboda duk wani abu da ake buƙata a wajen aikin nan an riga an samar da shi tun kafin a fara gudanar da aikin, kuma su kansu jaruman sun ba ni haɗin kai a matsayina na darakta.

Kuma Alhamdulillah, Ina alfahari da wannan fim ɗin da na kasance a matsayin mai bada umarni, domin duk wani aikin da ka yi kana son ka yi wanda ya fi shi, to haka nake kallon wannan fim ɗin a kan aikin da na yi a baya, domin bambancin wannan fim ɗin da waɗanda na yi a baya, shi ne a yanzu nake yin sa, kuma a kullum mutum yana ƙara wayewa ne a kan aikin da ya sa a gaba tunanin mutum a kullum yana ƙaruwa, don haka bambancin yana da yawa kamar salo na labari da za ka gani idan kana aiki, ka yi na baya, kullum so ka ke ka yi wanda ya fi shi. Don haka wannan fim ɗin Ina son na ga ya zama ya yi fice a cikin finafinan da aka yi a wannan shekarar ba ma a Kannywood ba har ma a duniya bakiɗaya.”

Isa Ballo Ja wanda ake yi wa laƙabi da sunan Dattijon arziki, yana cikin jaruman da suka taka muhimmiyar rawa a fim ɗin, ya shaida mana cewa;

” To shi wannan fim ɗin a gaskiya an ɗaga daraja ta a cikin sa, domin an bani matsayin da babu wani furodusa da ya taɓa bani a Kannywood na matsayin Babban Jarumi da yake jan fim. Saboda na fito a matsayin wani babban attajiri kuma duk rigimar da ake yi a cikin fim ɗin, to a gidana ake yin ta, kuma a gaskiya aiki ne da nake jin daɗin sa, domin babu abin da nake so a cikin fim kamar a ba ni fim na mutuntawa da girmamawa. Ko da yake duk finafinan da nake yi daidai suke, amma akwai wanda ake ba ka roll ɗaya, biyu, akwai wanda ake ba ka wanda ba ka ma san yawan sa ba. To wannan yana daga cikin wato shekaru na kusan 70 da wani abu a yanzu aka yi labari aka ɗora dattijo mai shekaru mai yawa labarin, saboda an fi bai wa mata da yara labarin, kasancewar an fi yin labari a kan soyayya, to wannan fim ɗin ba na matashi ba ne na dattijo ne wanda a cikin fim ɗin ana rigima a cikin gidana kuma ni ne mai gidan daga farko har ƙarshe, wannan wani sabon salo ne da nake ganin ya canza akalar aikin masana’amtar Kannywood ta hanyar ci gaban labarin da kuma aiki. Don haka ya kamata a yanzu mutane su gane, labari ko kuma aiki a masana’amtar Kannywood ya tashi daga labarin soyayya ya koma matakin harkokin rayuwar yau da kullum da ake gudanarwa.”

Nura Mado shi ne mashiryin fim ɗin ‘Faliha and Falisha’. Kuma shi ma mun ji ta bakin sa a kan yadda aikin yake gudana, inda ya bayyana mana cewa, ” To gaskiya wannan aikin babu abin da za mu ce sai dai godiya ga Allah, domin ita harkar mutane in dai za ka tara mutane da yawa a waje guda dole sai an rinƙa samun matsaloli nan da can, amma hakan bai hana mun kai ga samun nasarar da muke buƙata ba. Domin ka ga babban ƙalubale da muka samu shi ne na yanayin garin damuna wanda wani lokacin kafin mu fara aikin ruwa zai zo ko kuma muna tsakiyar aikin, amma duk da haka cikin ikon Allah mun samu damar gudanar da aikin ba tare da mun tsallake wata rana da ba mu samu mun yi aikin ba, kullum muna aikin, ga kuma shi Darakta Isah Alolo daman jajirtacce ne. Don ka ga a yadda muka tsara aikin za mu yi sati biiyu ne kuma cikin yardar Allah za mu kammala shi ba tare da an ƙara lokaci ba, don muna sa ran za mu kammala ma kafin lokacin da muka ɗauka.”

Timmah Makamashi, ita jarumar da ta fito a matsayin uwa a cikin fim ɗin Faliha and Falisha’, ta bayyana mana cewa, ” Gaskiya matsayin da aka ba ni a matsayin uwa a wannan fim ɗin ya burge ni, domin shi kan sa daraktan ya ce, na taka rawar gani kuma na bayar da gudunmawa a kan abin da ake so, don haka idan kiɗa ya canza rawa ma canzawa take yi, wannan ya sa nake ganin zan iya taka rawar gani a duk wani rol da za a ba ni, don haka wannan fim ɗin ya dace da zamani kuma a duk lokacin da ya fito ‘yan kallo za su gane hakan.”

Muhammad Hussaini wanda aka fi sani da Dan Lansi, shi ne manajan shirin fim ɗin ‘Faliha d Falisha’ ya shaida mana cewa, “A ɓangaren aikina a gaskiya an samu nasara, saboda muna aiki tare da darakta kuma su kansu jaruman sun ba ni haɗin kai yadda ya kamata a matsayina na mai kula da su, don haka duk wanda na kira ba na samun ɓata lokaci daga wajen sa, wannan ya sa aikin ya tafi yadda ake so, kuma ita kanta babbar furodusa ta ba ni damar gudanar da aikina yadda ya kamata, kamar yadda a can baya mun yi aikin fim ɗin ‘Akila’ da ‘Fanan’ ya yi fice, shi ma wannan fim ɗin da yardar Allah sai ya fi su karɓuwa saboda aikin na sa na an yi shi da ƙwarewa fiye da wanda aka yi a wancan, don haka muna sa ran fim ɗin zai je fiye da inda muke zato.”

Mansurah Isah, ita ce Babbar Furodusa, a cikin tattaunawar mu ta ita, ta bayyana cewa, “Bayan fim ɗin ‘Fanan’ da ‘Akila’ da muka yi, mun ɗan kwana biyu ba mu yi fim ba, sai a wannan lokacin da muke aikin fim ɗin ‘Faliha and Falisha’ duk da yake sunan za a ji da Turanci ne, amma fim ne na Hausa, saboda shi fim ne na ‘yan gayu shi ya sa muka zamanantar da sunan. Kuma shi wannan fim ɗin, a tunanin da nake, babu labarin da aka yi shi mai kamanni biyu a cikin harkar fim Kannywood sai wannan domin duk wanda zai kalli fim ɗin daga farko ba zai iya sanin mai zai faru a ƙarshe ba.

Ka ga na saba yin fim ya samu bambanci sosai da sauran finafinan da na yi a baya. Kamar fim ɗin ‘Akila’, fim ne na abin da ya faru da gaske, shi ya sa abin ya taɓa mutane har ma mutanen da suke da ya’ya suke jin tsoron yadda kulawar ya’yansu za ta kasance. Haka idan ka ɗauki fim ɗin ‘Fanan’ shi ma abubuwa ne da suka faru da gaske, shi ma sai ya samar da darasi ga mutane da yawa musamman waɗanda suke da matan da suke yi musu biyayya kuma suke wulaƙanta su. To shi wannan fim ɗin na ‘Faliha and Falisha’ ya ƙunshi abubuwan rayuwa kamar makirce-makirce da kuma irin yadda ake rayuwa ta cin amana.”

A game da kasuwar da ta tanadarwa fim ɗin kuwa cewa ta yi, “Muna sa ran za a haska shi ne a sinima, kuma za mu nemi wasu gidajen talbijin da mu ƙulla harkar kasuwanci da su ta hanyar sayen mallaka ko haskawa, kuma za mu saka shi a Youtube, da sauran guraren da zai kai ga jama’a domin Ina da burin fim ɗin ‘Faliha and Falisha’ ya isar da saƙon sa a ko’ina a cikin duniya, don haka Ina fatan Allah ya sanya albarka a cikin aikin ta yadda fim din Faliha and Falisha’ zai yadu a Duniya ya kai ga duk wani waje da ban yi zaton zai kai ba.”

By ukarofi