Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Kwamishinan Wasanni da Matasa na Jihar Kano, Mustapha Rabiu Kwankwaso ya nuna rashin gamsuwarsa game da gyaran Filin Wasa na Sani Abacha dake ƙofar Mata.
Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso a wata tattaunawa da ya yi da ‘yan jarida ya ce, babu shakka akwai kura-kurai wajen gyara filin wasan wanda ya jawo hankali akan hakan tun da fari.
Ya buƙaci Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da ya kafa wani kwamiti da zai binciki yadda aka yi aikin domin gano gaskiyar abinda ya faru.
Ya ƙara da cewa wannan gyara da aka yi mataki na farko ne akwai sauran ayyuka da suka haɗa da gyara wajen gudu na filin da wajen zama na manyan baƙi da ofishin ma’aikata dake filin wasan.
Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi wasu marasa kishin jihar Kano da yi wa ƙungiyar kwallon ƙafa ta Kano Pillars zagon ƙasa domin a ɗauke ta daga jihar Kano.
Kwamishinan matasa da wasannin na jihar Kano Mustapha ya jinjina wa Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf bisa nuna kulawa da yake yi ga ƙungiyar da kuma ci gaban matasan Jihar Kano.
