Al’ummar Minjibir sun karrama mai shari’a Hauwa Lawan ta babbar kotun Jihar Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Mai Shari’a ta Babbar Kotun Jihar Kano, Hauwa Lawan Umar Minjibir ta nuna farin ciki da gode wa Allah bisa zaɓo su da ƙungiyar” Minjibir Solidarity Forum’ ta yi ta karrama su, wanda hakan a cewarta ba dabara ko hikimarsu ba ce, horewa ce ta Ubangiji suna gode masa da wannan karamci da ƙungiyar da take haɗa zumunci da haɗa kan al’ummar Minjibir ta yi musu.

Ta bayyana hakan ne da take zantawa da manema labarai bayan karɓar shaidar karramawar da aka gudanar a Minjibir. 

Ta ce yadda aka ɗauke su abin misali aka yaba aka nuna domin yan baya ma su yi koyi da shi, suna  gode wa iyayensu da sune suka ba su tarbiyya da ilimi har suka samu wannan dama har ake yi musu wannan karramawar. 

Ta ƙara da cewa wannan karramawar ya daɗa musu ƙwarin gwiwa da karsashi na yin riƙo da gaskiya da amana. Da kuma adalci da yin komai bisa aiki da ilmi da bin doron doka musamman a matsayinta na masu yin hukunci duk abinda ya kama na adalci idan ya zo gabanta za su yi, suna kuma addu’ar Allah ya yi musu jagoranci a kai.

Mai shari’ar ta babban kotun jihar Kano, Hauwa Lawan Umar Minjibir ta yi kira ga al’ummar Minjibir su dage da yin ilimi da riƙo da addini da riƙe amana da waɗannan abubuwa guda uku babu inda mutum ba zai je a matakin rayuwa ba da yardar Allah.

By ukarofi