Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana damuwarsa kan yadda jam’iyyar APC mai mulki ta kasa iya tunkarar ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
Ya kuma zargi jam’iyya mai mulki da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da yunƙurin ruguza jam’iyyun adawa a ƙasar nan.
Yayin da ya ke bayyana ra’ayinsa game da haka jam’iyyun adawa ke ciki, El-Rufai ya ce tsari da ingancin shugabanci a Nijeriya na cikin halin ha’ula’i a ƙasar.
El-Rufai wanda da shi aka kafa jam’iyyar APC, ya bayyana hakan a yayin wani taro kan karfafa dimokraɗiyya a Nijeriya a Abuja a ranar Litinin.
Ya ce: “Ba na ɗaukar APC a wata jam’iyya. Babu wani ɓangare na am’iyyar APC da ya yi taro tsawon shekaru biyu. Babu komi, babu kwamitin ƙoli, babu komai. Sai dai bamu sani ba ko mutum ɗaya ne ya mamaye komai,” inji shi.
