Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Hon. Ɗalhatu A.A Bichi Ɗan Yalo, Mataimaki na musamman kan harkar fansho ga Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa tausayi da son kowa a biya shi haƙƙinsa da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabiru Yusuf yake da shi, ya sa ya ware zunzuruntun kuɗi har Naira biliyan 16 don biyan tsofaffin ma’aikatan gwamnatin jihar Kano da suka kammala aikinsu, ko kuma suka rasu akan aiki, gwamnan ya ga ya dace a biyasu bayan shekaru takwas da gwamnatin da ta gabata ta kasa taɓuka komai na biya tsofaffin ‘yan fashon haƙƙinsu, amma zuwan Gwamna Abba ƙasa da shekara biyu ya ware wannan kuɗi, kuma an biya ‘yan fansho da dama haƙƙinsu kuma wannan gwamnati ba ta tsaya ba, ta nan ta na cigaba da biyan ‘yan fansho na garatuti na waɗanda suka yi ritaya, har ma da magada da iyayensu suka kwanta dama duk ana cigaba da ba su haƙƙinsu tun daga zuwan wannan gwamnati har nan da shekara takwas da mu ke nema a wajen Allah, wannan gwamnati za ta yi a cewar Hon. ɗalhatu A.A Bichi, wanda aka fi sani da ɗan Yalo, da y abayyana wa manema labarai a birnin Kano.
Haka kuma ya ƙara da cewa bayan rantsar da gwamnan Kano, babu daɗewa ya ware biliyan biyar aka biya ‘yan fansho a karon farko, haka kuma ya sake ware biliyan biyar aka biya ‘yan fansho haƙƙinsu duk da lokacin ‘yan hamayya sun kai wannan gwamnatin ƙara na burinsu a ƙwaci gwamnati a basu, hakan bai hana Gwamna Abba wannan aiki ba, da sauran ayyuka na cigaban Kano da gwamna ya fara tun daga hawansa har zuwa yanzu, sai kuma gashi a wannan lokaci ya ware biliyan shida ana ta biyan waɗanda su kai ritaya haƙƙinsu, kuma wasu suna siyan gidaje, wasu kuma suna hidimar auren ‘ya’yansu cikin farin ciki wanda wannan ta sa gwamna Abba da mataimakinsa da sauran jami’an gwamnati da al’ummar Kano masu kishin talaka na farin ciki da wannan biyan haƙƙi na ‘yan fansho da kuma ayyukan da gwamnan Kano yake yi na cigaban Kano ta kowacce fuska, musamman ilimi lafiya hanyoyi, noma, ruwan sha, bai wa mata jari, tallafawa matasa da ayyuka da sana’o’i da dai sauransu.
A ƙarshe Hon. ɗalhatu A.A Bichi, ya kira ga shugabanni a kowane mataki da su yi koyi da gwamnan Kano wajen tausayawa al’umma a kowane lamari kuma jami’an gwamnati da al’ummar Kano da Nijeriya, su cigaba da addu’a da ba da haɗin kai ga gwamman Kano da kuma jagora Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Uba ga wannan gwamnati ta Kano.
