Daga BELLO A. BABAJI
A karon farko a tarihin ƙwallon ƙafa, Hukumar FIFA ta na shirin tabbatar da ƙasar Saudiyya a matsayin wadda za ta jagoranci gudanar da wasannin Kofin Duniya na shekarar 2034.
Haka ma ƙasashen Morocco da Sifaniya da Portugal za su jagoranci gudanar da gasar ta shekarar 2030.
Za a gudanar da batun tabbatar da ƙasashen a matsayin waɗanda za su jagoranci wasannin a yayin zaman FIFA, amma hakan ba zai sauya su matsayinsu ba kasancewar babu wasu ƙasashen da ke gogayya da su wajen neman riƙe jagorancin.
FIFA ta bada damar zaɓo ƙasa daga Nahiyoyin Asia da Oceania ga na 2026 inda ake sa ran daga Arewacin American za yi wasannin.
Bai wa Saudiyya wannan dama zai sa lamarin ƴancin ɗan-adam ya zama babban batu, kamar yadda ya faru shekaru biyu da suka gabata a ƙasar Ƙatar.