
Daga BELLO A BABAJI
A ranar Laraba ne Majalisar Wakilai ta yanke gudanar da bincike game da zargin ayyukan fasa-ƙwauri da cin zarafi daga wani jami’in Hukumar Kwastom (NCS).
Majalisar ta yi hakan ne a yayin zama tsakanin ƴaƴanta da aka saba, a lokacin da ɗan Majalisa Mista Oluwaseun Whingan daga Jihar Legas ya gabatar da ƙudirin al’umma na gaggawa.
Ɗan majalisar ya bayyana yadda gidajen jaridu daga kafafen sadarwa da Sahara Reporters suka ruwaito yadda aka yi fasa-ƙwaurin wasu motoci sama da 2,000 waɗanda ke ɗauke da shinkafa a yankin Badagry, akan idon jami’an Kwastom.
Ya ƙara da cewa wani bidiyo da ɗan jaridar binciken ƙwaf, Fisayo Soyombo ya fitar, ya bayyana hujjar da ke nuna jami’an suna da hannu a acikin haramtattun ayyukan.
Ya kuma bayyana yadda wani al’amari da ya faru a ranar 1 ga watan Disamba, 2024, inda aka ga wasu jami’an Kwastom da haɗin-gwiwar sojoji suna cin zarafin wasu matafiya guda biyu (Taofeek Olatubosun da Tafiya Abdelmalik).
Har’ilayau, ɗan majalisar ya ƙara da cewa, fasa-ƙwauri aiki ne da ke barazana ga tattalin arziƙin ƙasa ta hanyar illa ga kuɗin shiga da gwamnati ta ke samu da kuma nakasa masana’antu da sauransu.
Daga nan ne Majalisar ta umarci kwamitinta kan lamuran Kwastom da Tsaro da ya yi bincike game da lamarin tare da kawo mata rahoto a kai nan da makonni shida.
