Abdul Maikwashewa ya zama Shugaban Kwamitin Yaƙin neman zaɓen Tinubu na Kannywood

Daga AISHA ASAS a Abuja

Sanannen abu ne cewa, fim da masu yin fim na ɗaya daga cikin waɗanda ke matuƙar tasiri a rayuwar al’umma ta ɓangaren kwaikwayo da kuma samun soyayyar jama’a. Da yawa sukan ɗauki maganar jaruman finafinai fiye da ta shuwagabanni da makalamtansu, wannan ce ta sa suka zama a layin farko a duk lokacin da ake fatan wayar da kan al’umma ko kuma tusa masu ra’ayi ko soyayyar wani abu.

Dalilin kenan da ya sa a ɓangaren siyaya suke da muhimmiyar rawa da suke takawa, don haka duk wani ɗan siyasa da ke neman nasara zai nemi goyon bayansu don samun damar su tallatashi ga masoyasansu wanda hakan na da tasiri matuƙa.

Masana’antar Kannywood ita ce mafi sani da bunƙasa a duk masana’ansun finafina da ke Arewacin Nijeriya. Yawa, ƙwarewa da tasirin su ya sa suka zama a layin farko a duk lokacin da aka yi zancen neman masu shirya finafinai a Arewacin Nijeriya.

Biyo bayan irin tarba da kuma nishaɗantarwa da ɗan takarar shugaban ƙasa a Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya samu daga kaso mafi rinjaye na masana’antar ta Kannywood yayin ziyarar neman goyon baya da ya kai Jihar Kano, an fitar da sanarwar naɗa kaso mafi rinjaye na masana’antar Kannywwod a kwamitin yaƙin neman zaven Tinubu/Shatima.

Sanarwar ta ce, Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaven Shugaban Ƙasa na APC kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya amince da naɗin masana’antar shirya finafinai a Arewacin Nijeriya, Kannywood a matsayin mamba a kwamitin PCC, inda Furodusa Abdul Amart Maikwashewa ya kasance wanda zai jagoranci kwamitin.

Naɗin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren Yaɗa Labarai da mu’amala da jama’a ga Gwamnan Lalong, Dr. Makut Simon Macham, kuma mai ɗauke da kwanan wata 8 ga Nuwamba, 2022.

Sanarwar ta ce, naɗin ya biyo bayan tabbacin da ɗan takarar shugaban ƙasa a APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bai wa masana’antar ta Kannywood yayin wani taro da ya halarta a Kano inda ‘yan masna’antar suka tabbatar masa suna tare da shi.

Bayan baje fasaharsu da ‘yan Kannywood ɗin suka yi a gaban ɗan takarar a wannan rana, ya sa ya yi musu alƙawarin samar musu gurbi a Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa don tallafa masa wajen cimma burinsa na shugabancin ƙasa.

Shugaban PCC, Gwamna Simon Lalong, ya buƙaci ‘yan masana’antar su tattaro masoyansu don a haɗu a mara wa ɗan takararsu baya, tare da kira gare su da su ba da himma wajen tallata Asiwaju da manufofinsa ga ‘yan ƙasa yadda ya kamata.

‘Yan tawagar Kannywood ɗin sun haɗa da Abdul Moh’d Amart (Maikwashewa) a matsayin Babban Darakta da Ismail Na’abba Afakallah a matsayin Mataimakin Darakta, Jadda Garko a matsayin Mataimakin Darakta ta Biyu, sai Sani Mu’azu a matsayin Sakatare.

Sauran sun haɗa da; Malam Khalid Musa wanda ya kasance mai ba wa gwamnan Jihar Kano shawara kan harkokin masana’antar finafinai ta Kannywood ya zama mai bada shawara a wannan kwamiti na yaƙin neman zaɓe a Jihar Kano.

Yayin da Bala Ahmad ya zama takwaransa. Shu’aibu Yawale shi ma na ɗaya daga cikin sunanen da aka fitar a layin masu bada shawara ga kwamitin na Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC a Kano.

Jarumi Ali Nuhu ne aka zaɓa a matsayin Darakta a ɓangaren jarumai, Jamila Nagudu ce mataimakiyar sa ta ɗaya, shi kuwa ɗan wasan barkwancin nan Sulaiman Yahaya, wanda aka fi sani da Bosho mataimakin Darakta na biyu.

Shahararriyar mawaƙiya Fati Nijar na ɗaya daga cikin zaɓɓaɓu a wannan yaƙin neman zaɓen Tinubu, inda aka bayyana ta a matsayin mataimakiyar Darakta ta ɗaya a ɓangaren waƙa, Ado Gwanja ne mataimaki na biyu a wannan ɓangare. Ɗan Isa Mai Kaho mataimakin darakta na uku duk a ɓangaren na waƙoƙi.

Jarumin barkwanci kuma mai ba wa gwamnan Jihar Kano shawara Mustapha Badamasi Naburaska ne aka rattaba a matsayin Daraktan shirye-shirye. Shi kuma jarumi Alasan Kwalle ya zama mataimakin sa a wannan ɓangare.

Ahmad Salihu Alkanawy Darakta Tsare-tsare, Emanuel ne mataimakin sa. Tahir I. Tahir shi ne Sakataren shirye-shirye, jarumi Adam A Zango ne mataimakin sa na ɗaya, shi kuma Dailo Pam Lojok mataimakin Sakataren shirye-shirye na biyu.

Marubuci, mai shirya finafinai kuma editan jaridar Manhaja ta kamfanin Blueprint, Nasir S. Gwangwazo, ne aka naɗa Sakataren Yaɗa Labarai, Hafsat Sulaiman daga Jihar Kaduna ta zama mataimakiyarsa.

Hassan Shehu Kano ne Kodinetan Yaɗa Labarai na gidahen Jaridu, Rediyo da Talabijin. Ibrahim Adamu Ko’Odineta Yaɗa Labarai a Kafafen Sada Zumunta, inda za su taimaka wa Gwangwazo.

Malam Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) shine Daraktan Kula da Ayyukan Fasaha, Hamza baban Muri ya zama mataimakin sa na ɗaya, Ibrahim Maishunku kuwa ya kasance mataimaki na biyu a wannan ɓangaren.

Ɗan Musa Gombe ne Kodineta na harkokin cikin sitidiyo, yayin da Sulaiman Albankudi ya zama Kodineta na shirye-shirye. Shi kuwa Auwal BigTime a ɓangaren aka sanya sunansa a matsayin mataimakin Kodinetan.

Jaruma Mansura Isa ce Jami’ar walwala da jin daɗi, Nuhu Abdullahi ne aka naɗa a matsayin mataimakin ta na ɗaya, yayin da Abubakar Ndako Kutugi ya samu matsayin mataimaki na biyu.

Shi kuwa darakta Sadiq N. Mafia an ba shi muƙamin Manajan Shirye-shirye, Audu Sitin mataimaki na ɗaya, Audu Boda mataimaki na biyu.
Jaruma Asma’u Sani ce aka ba wa muƙamin Kodineta ta mata a yaƙin neman zaɓen ta ɗaya, Maijida Minna ta biyu.

Jarumi Sadiq Sani Sadiq, mai kula da tafiya-tafiye, Bello Muhammad Bello ne aka ba wa muqamin mataimaki. Shi kuma jarumin barkwanci Falalu A Ɗorayi an ba shi muƙamin Daraktan Kuɗi, Shatima Mansoor ne mataimakin Daraktn Kuɗi. Amina Adamu ce Shugabar Gudanarwa ta wannan tafiya, Ibrahim A.I.T mataimakin shugabar gudanarwa.

Lissafin bai tsaya a iya nan ba har sai da ya kawo jerin wasu sunayen da aka sanya sunayensu a matsayin dattijai na wannan tafiya ta yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inwar Jam’iyyar APC, wato Asiwaju Bola Ahmed Tinubu don su ma a amfana da ta su irin baiwar, shawarwari da kuma ƙuri’um masoyansu. Sunayen sun haɗa da; Sani Idris Moɗa, Magaji Ibrahim Mijinyawa, Muhammad B. Uwar Hankaka, Hajara Usman, Sa’idu Isa Gwaja da kuma Ɗan Azumi Baba, wanda kuka fi sani da Kamaye.

Tinubu tare da ‘yan Kannywood

Haka zalika an bayyana wasu sunayen da suke mamba na wannan tafiya, a cikin sunayen akwai jaruma Maryam Yahya, Husaini Sule Koki, Nura Ɗan Dolo, wato Ɗanƙwambo, Aminu Ari Baba, Fati Abubakar Das, Nazifi Shariff, Abubakar Sulaiman wanda aka fi sani da Ɗan Auta, Umma Shehu, Yahanasu Sani, Hawa Abubakar, wato Hawa Waraka, Aminu Mirrow, Waziri Dabo, Anas Sulaiman Nasir, Sani Ɗangwari, Bala Kufaina Abuja, Hamza Badamasi, Hadiza Abdullahi Kabara, Aminu Dumbulum, Maimuna Abubakar wadda aka fi sani da Momi Gombe, Hawa Garba, wato ‘Yar Auta. Aisha Mahuta, Musa Mai Sana’a, Binta Ola, Abdulrahman Alfazazee, Nasir Adam Salih, Adamu A.D Bauchi, Mudassir Kassim da kuma Tijjani Abdullahi Asase.

Tuni dai Majalisar Dattawan Kannywood (Kannywood Elders Forum) ta hannun Jami’in Yaɗa Labaranta, Kabiru Maikaba, ta taya Abdul Maikwashewa murya tare da sauran mambobin kwamitin, tana mai yi musu fatan alheri da masana’antar ta Kannywood bakiɗaya.