Kasafin 2023: Naira biliyan 871.3 ba za ta ishi ‘yan sanda ba – Minista

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Harkokin ‘Yan Sanda, Mohammed Dingyadi ya ce Naira biliyan 871.3 da aka ware domin gudanar da ayyukan ‘yan sanda a cikin kasafin kuɗin 2023 ba zai isa ba.

Dingyaɗi ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Talata lokacin da ya ke jawabi a taron kare kasafin kuɗin shekarar 2023 wanda kwamitocin majalisar dattawa da na wakilai na majalisar dokokin ƙasar kan harkokin ‘yan sanda su ka gudanar.

Ministan ya ce kasafin kuɗin da aka ware wa ma’aikatar da hukumominta domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ba zai isa ba.

Dingyaɗi ya ce daga cikin jimillar Naira biliyan 871.3 da aka ware a kasafin kuɗin shekarar 2023, Naira biliyan 3.52 na ayyukan babbar ma’aikatar ne.

Ya ce an ware wa rundunar ‘yan sandan Nijeriya Naira biliyan 805.5.

Ministan ya ce makarantar horar da ‘yan sanda za ta samu Naira biliyan 5.17, yayin da asusun kula da ‘yan sandan Nijeriya ya samu Naira biliyan 57.14, wanda ya kai Naira biliyan 871.30.