2023: Gobe INEC za ta fara bajekolin rajistar zaɓe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta ce, za a fara bajekolin rajistar masu kaɗa ƙuri’a a gobe Asabar.

Festus Okoye, Kwamishinan INEC na Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Kaɗa Ƙuri’a na Hukumar, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya a jiya Alhamis.

Ya bayyana cewa, a taronta na mako-mako da aka gudanar a ranar Alhamis 10 ga Nuwamba, 2022, hukumar ta tattauna akan nuna gabaɗaya rajistar masu kaɗa ƙuri’a na ƙasa bakiɗaya, don sauraron ƙorafe-ƙorafe daga ’yan ƙasa, kamar yadda doka ta tanada tare da amincewa da tsarin gudanar da zaɓen.

Ya ce, “kamar yadda hukumar ta sanar a baya, za a buga dukkan rajista mai ɗauke da masu rajista 93,522,272, inda za a ɗauki jiki makonni biyu, daga 12 zuwa 25 ga Nuwamba, 2022.

“Za a nuna kwafin rajistar a dukkan mazaɓu 8,809 da kuma ƙananan hukumomi 774 a faɗin ƙasar. A karon farko, za a kuma buga kwafin yanar gizo na gabaɗayan rijistar akan gidan yanar gizon Hukumar (ziyarci www.inecnigeria.org/display_register kuma bi umarnin).

“Rijistan za ta bayar da suna, hoto, ranar haihuwa da kuma lambar tantance masu kaɗa ƙuri’a (VIN) na kowane mai rajista.

Kwamishinan ya cigaba da cewa, ana iya samun cikakken bayani kan matakai da hanyoyin gudanar da aikin, gami da fom ɗin da suka dace daga jami’an Hukumar a wuraren da aka bajekolin a wuraren rajista (Wards) da Ƙananan Hukumomi.

“An kuma shigar da bayanan a shafin hukumar da shafukan sada zumunta. A bisa tanadin doka, tsaftace rajistar masu kaɗa ƙuri’a wani nauyi ne na ƙasa baki ɗaya.

Ya zuwa yanzu, Hukumar ta kori waɗanda ba su cancanta ba ta hanyar amfani da Tsarin Shaida na Halitta (ABIS).

Ta hanyar yin aiki tare da ’yan ƙasa, za mu iya ƙara tsaftace rajistar saboda ita ce muhimmin ginshiƙi na ingantaccen zaɓe,” inji Okoye.