Abin da ya sa muka gamsu da manufofin Kwankwaso – Matasan Arewa a Legas

Daga WAKILINMU

Shugaban Gamayyar Matasan Arewa Mazauna Jihar Legas, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci ya bayyana cewa, sun gamsu da manufofin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa yadda suka ƙunshi dabarun magance manyan matsalolin da suka addabi Nijeriya a zamanin nan.

A cewar Galadanci, lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su zabura su tabbatar da nagarta wajen zaɓen shugabannin da suka cancanta a 2023 domin fita daga halin da suke ciki na rashin tsaro da tsadar rayuwa.

Ya ƙara da cewa, “Ƙungiyarmu ta Gamayyar Matasan Arewa a Legas, mun fahimci manufofin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso kuma mun gamsu da jawabinsa da ya yi wa al’ummar Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.

“Abin da ya fi ɗaukar hankalinmu a jawabin nasa shi ne idan Allah ya ba su ikon cin nasara a zaɓen 2023, ya ƙudiri aniyar magance matsalolin tsaron Nijeriya da iyyakokinta, musamman ƙudirin da ya yi na zai ɗauki sojoji kimanin miliyan ɗaya da ‘yan sanda miliyan ɗaya da sauran jami’an tsaro waɗanda za a tantance su tun daga matakin ƙaramar hukumarsu har zuwa jiha, yin hakan babbar nasara ce ga ƙasarmu da kuma ‘yan ƙasa baki ɗaya.

“Sannan da batun bunƙasa harkar ilimi da sauran tsare-tsare na alheri wanda waɗannan maganganu su ne suka ba mu damar mu taya su da addu’o’inmu na alheri a kan Allah ya cika musu burinsu mu samu zaman lafiya da ci gaban al’umma.

“Ƙasarmu mun san yadda Allah ya yi mata arzikin ma’adinai masu daraja waɗanda muna ji muna gani wasu na yi mana kisan gilla, suna amfani da wannan damar suna kwasar dukiyar.

“Sun haɗa baki da baƙin haure an hana mu zaman lafiya. Don haka wannan lokaci ne da za mu fito domin ganin an daina yi wa al’ummar Nijeriya wasan wawaso da dukiyar da Allah ya bayar ga ƙasar domin al’ummar Nijeriya su amfana.

“Ba kuɗi za a ba mu ba domin muna dimokraɗiyya ne a yanzu, ya kamata mu tashi tsaye mu kawo wa ƙasarmu ci gaban da za mu yi alfahari da ita a matsayin Nijeriya ƙasa ɗaya mai al’umma ɗaya da ke samun bunƙasa.

“Muna kira ga ‘Yan Nijeriya a kan su fahimci cewa abin da muka fi buƙata a wannan zaɓen na 2023 da za a yi shi ne mu yi watsi da harkar ubangida, kowane ubangida yana da wani muradin kansa a fagen siyasa kuma wannan muradin ba don kishin ci gaban jama’a ba ne sai dai ci gaban kansa da iyalansa.

“Don haka wannan ne lokaci mafi dacewa da za mu yaƙi azzalumai waɗanda ana yi mana kisan gilla ba dare ba rana amma ba su damu ba, yadda za su ci gaba da mulki da ɗora nasu a kai kawai suke ƙoƙarin yi saboda sun mayar da mulkin ƙasar ya zama na gado.” In ji shi.

Ya ƙara da cewa, yadda aka riƙa sayen wakilai masu zaɓe tun daga zaɓen fitar da gwani, manuniya ce ta neman ƙara danne talakan Nijeriya.

“A idon duniya manyan ‘yan takara suka dinga sayen wakilai masu zaɓe da ake ce wa ‘delegate’ domin su ci gaba da kassara mu. Talakan Nijeriya ya san irin uƙubar da yake ciki. Don haka muna ƙara yin kira ga shugabannin manyan ƙasashe na duniya, matuƙar suna son ɗorewar dimokuraɗiyya a Nijeriya, su taimaka wajen tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya ne suka zaɓi waɗanda suka cancanta da za su fitar da su daga halin da ƙasar take ciki. Duk wani ɗan ƙasa nagari da ka sani ya gaji da kisan gilla da tsadar rayuwa.

“Mu a matsayinmu na gamayyar matasan arewa da ke Legas, muna kira ga dukkan ‘yan ƙasa ba tare da bambancin ƙabila ko addini ba, mu tashi tsaye mu zaɓi cancanta, wannan ne kaɗai zai kai mu ga tudun mun tsira a 2023,” a cewarsa.