Xi Jinping zai halarci taron ƙolin G20 da na APEC tare kuma da ziyara a Thailand

Daga CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Madam Hua Chunying, ta sanar a yau Jumma’a cewa, bisa gayyatar da takwaransa na ƙasar Indonesiya Joko Widodo ya yi masa, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping zai isa tsibirin Bali na ƙasar Indonesiya, don halartar taron ƙolin ƙungiyar ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki na G20 karo na 17, wanda zai gudana daga ranar 14 zuwa 17 ga watan da muke ciki.

Haka kuma, bisa gayyatar da firaministan ƙasar Thailand Prayuth Chan-ocha ya yi, shugaba Xi zai isa birnin Bangkok na ƙasar, tsakanin ranar 17 zuwa 19 ga wata, don halartar kwarya-ƙwaryar taron shugabannin ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Asiya da yankin tekun Pasific a fannin tattalin arziki ko APEC karo na 29, wanda zai gudana a ƙasar Thailand, kana zai gudanar da ziyarar aiki a ƙasar.

Ana sa ran shugaba Xi zai gana da takwarorinsa na wasu ƙasashe, yayin ziyararsa ta wannan karo, waɗanda suka hada da Emmanuel Macron na Faransa, da shugaba Joe Biden na ƙasar Amurka, da Macky Sall na ƙasar Senegal, da dai sauransu.

A yayin taron manema labaru da aka saba gudanarwa a wannan rana, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana fatan ƙasar Sin, game da halartar ayyukan da shugaba Xi Jinping zai gudanar.

Game da taron ƙolin G20 na tsibirin Bali, Zhao ya ce, wannan shi ne karo na farko da shugaban ƙasar Sin zai halarci taron koli na ɓangarori da dama, tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20.

Ya ce a halin yanzu, duniya na fuskantar ƙalubale a fannin samun ci gaba, kuma a matsayinsa na babban dandalin haɗin gwiwar tattalin arziki na ƙasa da ƙasa, ya kamata ƙungiyar G20 ta ƙarfafa haɗin kai, tare da daidaita manufofin tattalin arziki, da yin ƙoƙari tare, don neman dauwamamman ci gaban tattalin arzikin duniya yadda ya kamata.

Game da ƙwarya-ƙwaryar taron kolin na APEC, Zhao ya ce, APEC wani muhimmin dandali ne na hadin gwiwar tattalin arziki a yankin Asiya da tekun Pasifik.

Kuma shugaba Xi Jinping zai gabatar da muhimmin jawabi a gun taron, inda zai yi cikakken bayani kan muhimman manufofin ƙasar Sin, game da zurfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Asiya da tekun Pasifik, da sa kaimi ga bunƙasuwar tattalin arzikin yanki da na duniya baki ɗaya.

Zhao ya ƙara da cewa, “Muna sa ran dukkan ɓangarorin za su amince da ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Asiya da tekun Pacific, tare da sanya sabon kuzari ga ci gaban tattalin arzikin yankin, har ma da dukkanin duniya.”

Mai fassara: Bilkisu Xin