Bikin CIIE na haifar da moriya ga duniya

Daga CMG HAUSA

Alƙaluman da aka fitar dangane da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasuwannin ƙasar Sin (CIIE) karo na 5 sun nuna cewa, akwai ƙasashe da yankuna, da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa kimanin 145 da suka halarci bikin.

Kana, wasu kamfanoni fiye da 2800 na ƙasashe da yankuna 127, sun nuna sabbin kayayyaki da fasahohi kusan 438, adadin da ya dara na bikin bara.

Ban da wannan kuma, darajar kwantiragin da aka ƙulla wajen bikin, wadanda za a aiwatar da su cikin shekara mai zuwa, ta kai dalar Amurka biliyan 73.52, jimilar da ta ƙaru da kashi 3.9% bisa ta bikin bara.

Wannan sakamako ya shaida muhimmancin bikin CIIE, musamman ma a fannonin ƙarfafa tunanin buɗe ƙofa ga ƙasashen ƙetare, da samar da kayayyakin da za su amfani al’ummun duniya.

Haka zalika, a yayin bikin CIIE na wannan karo, an samar da rumfuna kyauta ga kamfanonin ƙasashe marasa karfin tattalin arziki. Wannan ya taimaka wajen baje kolin kyashu din ƙasar Guinea Bissau, da barguna ƙirar ƙasar Afghanistan, da sauransu, waɗanda aka nuna su tare da kayayyaki masu fasahohin zamani na ƙasashe masu sukuni.

Hakan ya nuna yadda ake ƙoƙarin tabbatar da adalci da daidaito tsakanin al’ummun ƙasashe daban daban.

Yanzu haka, an riga an ƙaddamar da aikin sanin kamfanonin da suke sha’awar halarta bikin CIIE na gaba, inda wasu kamfanoni da ƙungiyoyi kimanin 60 sun riga sun sa hannu don tabbatar da aniyyarsu ta halartar bikin.

Ba shakka bikin CIIE zai ci gaba da samar da moriya ga al’ummun duniya a nan gaba.

Mai fassara: Bello Wang