Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 200 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau.

Sama da ‘yan bindiga 200 ne sojoji suka kashe a dajin Gando da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara.

Mazaunin yankin da ya bayyana sunansa Malam Garba Lawali Bukkuyum ya shaida wa Blueprint Manhaja ranar Juma’a a wata hira ta wayar tarho cewa, sojojin sun fara ba-ta-kashi da yanbindigar da suka addabi yankin a ranar Talata da Laraba da Alhamis din da ta gabata.

Malam Garba ya bayyana cewa sojojin sun tare ‘yan bindigar ne a lokacin da suka yi awon gaba da daruruwan shanu daga al’ummar Zuggu da ke ƙaramar hukumar Kebbe a jihar Kebbi.

A cewarsa, an kashe ‘yan bindigar ne a arangama daban-daban guda uku da suka yi da sojoji.

“A arangamar farko da aka yi a ranar Talata, an kashe ‘yan bindiga sama da 100, kuma a ranar Laraba da mutanensu suka yi yunƙurin zuwa su kwashi gawarwakin mutanen da suka mutu, an kashe da dama daga cikinsu, sannan a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, sun tattara mutanensu sun yi yunƙurin kwashe gawarwakin jama’arsu yayin da sojoji suka kai masu ƙazamin hari inda suka kashe daruruwansu nan take,” inji Malam Garba.

Ya ƙara da cewa, “Kamar yadda nake magana da kai a halin yanzu, ɗaruruwan mutane ne suka yi dafifi zuwa wurin da lamarin ya faru ciki har da ni, kuma mun gano cewa sama da ‘yan bindiga 200 ne sojoji suka kashe a yayin samamen.”

Ya bayyana cewa an ƙwato babura sama da sittin daga hannun ‘yan bindigar a yayin samamen da sojoji suka kai da suka ha daa da makamai da alburusai masu yawa.

Ya ce, “Ɗaruruwan shanu aka ƙwato daga hannun ‘yan bindigar kuma an tsare su a wurin aikin gona na ƙaramar hukumar Gummi da kuma ƙauyen Ɗaki Takwas da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum waɗanda sojojin suka kama a yayin samamen”.

Ya zuwa haɗa wannan labari, ƙoƙarin da wakilinmu ya yi don Jin tabakin kakakin rundunar Operation Hadarin Daji a Zamfara, Kyaftin Ibrahim ya ci tura.