Abin da ya hana jagororin ADC ganin El-Rufa’i yayin da yake tsare – ICPC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Yaƙi da Rashawa ICPC, ta ce ta hana shugabannin jam’iyyar ADC ziyartar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne saboda biyayya ga umarnin kotu da ya taƙaita damar ganin sa yayin da yake tsare a hannun hukumar.

A cewar Jaridar punch, kakakin hukumar John Odey ya bayyana cewa kotu ta amince ne kaɗai wa iyalansa na kusa, lauyoyinsa da likitocinsa su riƙa ganinsa a halin.

Ya kuma musanta zargin cewa jami’an tsaro sun tsorata shugabannin ADC a hedikwatar ICPC da ke Abuja, yana mai cewa abin da aka gani tsari ne na tsaro na yau da kullum.

El-Rufa’i na fuskantar tuhume-tuhume tara da suka shafi zargin cin hanci da karya dokokin gwamnati, amma ya musanta dukkan su a yayin shari’a.

Wannan bayani na zuwa ne sakamakon ƙorafi da jami’an ADC suk yi a ranar Juma’a cewa an hana su ganin tsohon gwamnan a hedikwatar ICPC da ke Abuja.

Waɗanda aka hana shiga ganin El-Rufa’in sun haɗa da Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Rauf Aregbesola, Sakataren yaɗa labarai, Bolaji Abdullahi, da kuma Sakataren yaɗa manufofin jam’iyya, Salihu Lukman.

By Babaji