Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Taƙaddama kan zargin da ke nasaba da badaaalar dala miliyan 21 (kimanin Naira Biliyan 34.65) na cin hanci ta mamaye Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC), inda ƙungiyoyin fararen hula kamar OilWatch Nigeria da Workers’ Rights Alliance suka buƙaci a kama Ojulari tare da gurfanar da shi a kotu.
Kungiyoyin sun danganta wannan buƙata da iƙirarin cewa wani da ake tsare da shi, Abdullahi Bashir Haske, ya amsa cewa Ojulari ne ya ba shi ajiyar kuɗaɗen.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar 31 ga Yuli a hedikwatar EFCC, gamayyar ƙungiyoyin fararen hula ta zargi Ojulari da cin amanar tattalin arzikin ƙasa.
Gamayyar ta kuma bayyana cewa rufe matatun mai da aka daɗe da yi da kuma shirin sayar da kadarorin NNPCL su ne maƙasudin zanga-zangar da suka yi.
Kungiyoyin sun fara zanga-zanga na kwanaki uku tun daga 1 ga watan Agusta a gaban Majalisar Tarayya, hedikwatar NNPCL da ofisoshin EFCC don tilasta gwamnati ɗaukar mataki.
Wasu ƙarin zarge-zarge sun bayyana cewa akwai wani tsarin karbar cin hanci na dala miliyan 21 tsakanin masu cinikin mai da kwangilolin bututun mai, wanda aka gano bayan Ojulari ya sauya tsarin karɓar kuɗaɗe a kamfanin.
Wani mai kwarmato ne ya sanar da EFCC waɗannan bayanai, wanda hakan ya sa aka toshe asusun da ake zargi da hannu a cikin badaƙalar.
Ba gaskiya ba ne rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai na yanar gizo ke yaɗawa cewa Bayo Ojulari, shugaban kamfanin NNPCL, ya yi murabus daga muƙaminsa.
Wani amintaccen majiyar Fadar Shugaban ƙasa ya bayyana wa manema labarai a ranar Asabar cewa wannan rahoto “ƙarya ne kuma sharri ne kawai.”
\Rahotannin sun yi zargin cewa hukumar EFCC ce ta tilasta wa Ojulari yin murabus daga kujerar shugabancin NNPCL.
Sai dai majiyar fadar shugaban ƙasa ta karyata wannan batu, tana mai cewa babu gaskiya ko kaɗan a cikin wannan iƙirari.
Shugaba Bola Tinubu ne ya naɗa Bayo Ojulari a watan Afrilu, 2025, tare da umarnin ya aiwatar da sauye-sauyen da za su ƙara inganta ayyuka, dawo da amincewar masu saka jari da kuma tabbatar da cewa NNPCL ta zama kamfani mai riba da tsari.
Kafin naɗin Ojulari, Shugaba Tinubu ya sallami tsohon shugaban kamfanin, Mele Kyari, da shugaban kwamitin gudanarwa na NNPCL, Pius Akinyelure, a wani ɓangare na ƙoƙarinsa na gyara harkokin kamfanin.
