
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Cibiyar Tabbatar da Gaskiya da Adalci ga Ƴancin Al’umma (SERAP) da Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE), sun shigar da ƙara akan Gwamna Umar Bago na Jihar Neja bisa zargin sa da barazanar rufe gidan rediyon Badeggi FM da ke zaman kansa a jihar.
A takardar, wadda aka fitar a ranar Juma’a, 8 ga watan Agusta, kuma aka miƙa a Kotun Tarayya da ke Legas, ɓangarorin sun nemi a yi wa gwamnan da NBC iyaka daga wulaƙantawa ko yi wa gidan rediyon barazana, ko ƙwace masa lasisi da ƙoƙarin tantance mai shi.
Haka kuma, sun nemi kotun ta yi bayani a dokance ko NBC na da haƙƙin bai wa gidan rediyon kariya daga cutarwa daga ɓangaren gwamnan.
Ɓangarorin sun kuma nemi kotun da ta bayyana ko NBC na da haƙƙin bada kariya ga Badeggi FM ko kuma sauran kafafen yaɗa labarai daga kowane irin barazana a Nijeriya.
Sannan, sun ce saɓa wa doka ne a ce gwamna ya yi yunƙurin lalata farfajiyar gidan rediyon da ƙoƙarin tantance mamallakinsa, wanda a cewarsu ƙoƙarin take ƴancin bayyana kai da ƴancin yaɗa labarai ne.
A kwanan baya ne gwamnan ya umarci a kwace lasisin aiki na gidan rediyon sakamakon zarginsa da ƙoƙarin tada hankalin al’umma akan gwamnatin jihar ta shirye-shiryen da ya ke yaɗawa.
