Rundunar sojan Nijeriya ta ce, babban taro na duniya wanda ita ma Nijeriya ta sanya hannu a kansa, bai yarda da kashe tubabbun ‘yan ta’addan da suka miƙa wuya ba.
Rundunar ta faɗi haka ne a matsayin martani ga ra’ayin wasu ‘yan ƙasa da ke ganin cewa me zai hana a kashe ‘yan Boko Haram ɗin da suka ce sun tuba maimakon amincewa da su su ci gaba da rayuwa a cikin al’umma.
MANHAJA ta kalato cewa a tsakanin watanni ukun da suka gabata, mayaƙan Boko Haram da na ISWAP sama da 3,000 ne aka damƙe ko suka tuba suka miƙa wuya ga rundunar “Operation Hadin Kai” mai yaƙi da ta’addanci a shiyyar Arewa-maso-gabas.
Wannan adadi ya haɗa har da mutum 1,009 da aka damƙe waɗanda daga bisani aka damƙa su ga Gwamnatin Borno ran 14 ga Yuli bayan an kimtsa su.
Rundunar sojin Nigeriya ta ce, sojojin da aka tura aiki ƙarƙashin shirin “Operation Haɗin Kai” sun karɓi mayaƙan Boko Haram/ ISWAP da suka miƙa wuya suka tuba daidai da dokar ƙasa da ƙasa kan sha’anin yaƙi.
Yayin tattaunawarsu da jaridar LEADERSHIP, daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Brig Gen Onyema Nwachukwu, ya ce mayaƙan sun miƙa wuya ne saboda irin ƙwararan matakan da aka ɗauka wajen yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa-maso-gabas.
Ya ƙara da cewa, ‘yan ta’addan sun zaɓi su yi watsi da gwagwarmayarsu duba da cewa gwagwarmayar tasu ba za ta haifar musu da wani amfani ba, don haka suka zaɓi zaman lafiya.
Haka nan, ya ce da alama ‘yan Boko Haram sun juya wa mayaƙan ISWAP baya hakan ya sa suka zaɓi su miƙa wuya, tare da cewa yadda suka miƙa wuya a Nijeriya haka ma za su kwatanta a duk inda suke a sauran ƙasashen yankin tabkin Chadi.