Rashin tsaro: INEC ta tsaida aikin rajistar zaɓe a ƙananan hukumomi 5 a Filato

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta dakatar da aikin rajistar masu zaɓe da ake yi a faɗin ƙasar nan a ƙananan hukumomi biyar na Jihar Filato.

A wata sanarwa da Madam Caroline Okpe, Sakataren Gudanarwa ta INEC, ta fitar a madadin Kwamishinan Zaɓe mai zama a jihar (REC), a ranar Litinin a Jos, ta ce an ɗage aikin ne saboda dokar hana zirga-zirga da gwamnatin jihar ta saka.

Ta ce, “Ɗage aikin zai shafi cibiyoyin rajistar a ƙananan hukumomin Barkin Ladi, Bassa, Jos ta Gabas, Jos ta Arewa da kuma Riyom har sai hali ya yi.

“INEC ta na tabbatar wa da sababbin masu zaɓe da waɗanda ke da matsala da katin su cewa za a yi masu aikin da zarar yanayin ya inganta.”

Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) ta ruwaito cewa an samu matsalar rashin tsaro ne a wasu sassa na garin Jos, wadda ta kai ga kisan gillar da aka yi wa wasu matafiya waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, a Hanyar Rukuba da ke cikin Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.

An ce matafiyan su na kan hanyar su ne ta dawowa daga taron Zikiri na shekara-shekara da ake yi a Bauchi lokacin da wasu mutane da ‘yan sanda su ka ce “‘yan iskan gari ne” su ka far masu.

Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnoni a faɗin ƙasar nan sun yi Allah-wadai da kisan gillar kuma sun yi kira ga jami’an tsaro da su gano waɗanda su ka aikata ta’asar.

Madam Okpe ta ce tilas ne INEC ta tsayar da aikin rajistar domin ba za ta iya ci gaba da shi ba saboda wannan matsala abar baƙin ciki ta rashin tsaro, wadda ta tilasta wa gwamnatin Jihar Filato ta saka dokar hana yawo ta awa 24 a Jos ta Arewa.

Haka kuma gwamnatin jihar ta ƙaƙaba dokar hana yawo daga ƙarfe 6 na yamma zuwa ƙarfe 6 na safe a ƙananan hukumomin Bassa da Jos ta Kudu saboda waɗannan hare-haren.

Madam Okpe ta ce INEC za ta tabbatar da cewa dukkan ‘yan ƙasa da su ka cancanta a jihar za a yi masu rajista idan halin da ake ciki ya gyaru.